Abin da ya sa mabiya addinai ba sa hakurin zama da juna a Najeriya

Abin da ya sa mabiya addinai ba sa hakurin zama da juna a Najeriya
An wallafa

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

A yayin da Najeriya ke shirin tunkarar babban zabenta na shekara ta 2023, wani batu da ke jan hankali shi ne tasirin da addini ka iya yi ga zaben.

A cikin shekara biyar da ta gabata an samu karuwar hare-hare kan mabiya addinin Musulunci da kuma kirista a kasar.

Shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari ya daura laifin irin wadannan hare-haren ne kan wadanda ya kira mutane dake yunkurin tada zaune tsaye da kuma kawo rarrabuwar kawuna.

To sai dai kuma wasu shugabannin addini na cewa akwai bukatar gwamnati ta kara ƙaimi wajen bai wa mutane dama su yi addinin da suka zaba da kuma magance kalaman kiyayya a Najeriya.