Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Pochettino ya ƙara shiga matsi bayan cin Chelsea 4-2 a ƙarshen mako
Mauricio Pochettino ya kara shiga cikin matsi kan makomarrsa a Chelsea, bayan da Wolves ta doke su 4-2 ranar Lahadi a Premier League.
Wasa na 31 da Pochettino ya ja ragama a kungiyar Stamford Bridge, iri daya da yawan da Graham Potter ya yi kafin a kore shi a bara.
An sallami Potter daga aiki, bayan wata shida yana horar da Chelsea, wanda ya ci wasa 12 da canjaras takwas da rashin nasara 11.
Shi kuwa Pochettino wasa 14 ya ci, amma rashin nasara iri daya da wadda Potter ya yi a Chelsea.
To sai dai ɗan kasar Argentina ya kai kungiyar wasan karshe a Carabao Cup, kofin farko da take fatan dauka tun bayan 2021.
To sai dai kamar an fara dawo wa daga rakiyar Pochettino, bisa halin da kungiyar take ciki, bayan da Todd Boehly ya kasa kamo bakin zaren duk da kashe kusan fam biliyan ɗaya wajen sayen sabbin ƴan wasa.
Wasan da Wolves ta ci Chelsea, shi ne karo na biyu a jere da aka zura kwallo hudu karkashin Pochettino, bayan da Chelsea ta yi rashin nasara 4-1 a tsakiyar mako.
An taba doke Chelsea da kwallo hudu a raga sau biyu a jere cikin Nuwamba, inda ta tashi 4-4 da Manchester City, sai Newcastle ta ci 4-1.
Rabonda a zura mata kwallo da yawa a raga a wasa biyu a jere a Premier League tun tana buga rukunin farko a Disambar 1989 lokacin da Wimbledon ta ci 5-2 da wanda QPR ta yi nasara 4-2 sai kuma Liverpool ta casa Chelsea 5-2.
A wannan lokacin an zura kwallo 43 a ragar Chelsea a wasa 31 kawo yanzu, iri daya da yawan wadanda aka ci kungiyar karkashin Potter a bara.
Haka kuma a ranar Lahadi Matheus Cunha ya zama ɗan wasa na hudu da ya ci Chelsea kwallo uku rigis a Premier League a Stamford Bridge.
Wadanda suka ci Chelsea kwallo uku rigis a gida sun hada da tsohon ɗan wasan Arsenal, Nwankwo Kanu a 1999 da Robin van Persie a 2011 da kuma ɗan wasan Manchester City, Sergio Aguero a 2016.