Yadda za ku kula da jikinku a lokacin hunturu

An wallafa

Yayin da ake bankwana da damunar bana hukumar hasashen yanayi ta Najeriya, NIMET, ta yi tsokaci game da karatowar yanayin hunturu.

Hukumar ta ce yanayin hunturun na tafe da matsaloli da sukan shafi lafiyar bil'Adama da muhalli da kuma harkokin yau da kullum.

Cikin wata hira da BBC, shugaban hukumar, Farfesa Mansur Bako Matazu, ya ce idan damuwa ta kusa zuwa karshe za a rinka ganin yanayi na sauyawa kamar idan an yi ruwa kuma sai aga kamar yanayi na sanyi.

Ya ce, hasashen hukumarsu ya hango cewa za a samu iska mai karfi na kadawa daga yankin arewa maso gabas, sannan kuma za a samu hazo da zai rage ganin da ake.

Farfesa Mansur Bako Matazu, ya ce, saboda irin sauyawar yanayin da za a fara fuskanta akwai shawarwarin da suke so sub a wa mutane don kula da kansu.

Ya ce, “ Da ya ke za a fuskanci hazo, mutanen da ke matsalolin da suka shafi numfashi dole su kiyaye, da kuma mutanen da ke da kan jiki suma dole su kula da kansu.”

Ya ce, a lokutan sanyi fatar jikin mutum na bushewa saboda kadawar iska da makamantansu, a don haka ya kamata mutane su rinka amfani da man da ba zai sanya fatar jikinsu ta rinka saurin bushewa ba.

Shugaban hukumar ta NIMET, ya ce, “ Itace da bishiyoyi da ciyayi da ma katakai na gidaje na bushewa, dole a kula saboda ana yawan samun gobara a lokacin hunturu, irin mutanen da ke lalurar da ta shafi numfashi kamar asma, yana da kyau su rinka amfani da magungunansu akai-akai, da kuma sanya abin rufe hanci idan za a fita.”