Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Za a yi hutu a Premier League domin ci gaba da FA Cup a karshen mako
Ranar Alhamis za a ci gaba da wasannin zagaye na uku a FA Cup, inda za a buga karawa da yawa, hakan na nufi za a yi hutu a Premier League a karshen mako.
Kawo yanzu an buga wasannin mako na 20 a babbar gasar tamaula ta Ingila, inda Liverpool ke jan ragama da maki 45, sai Aston Villa mai maki 42.
Manchester City ce ta uku da maki 40, iri daya da na Arsenal ta hudu.
Cikin wasannin FA Cup da za a ci gaba da karawar har da fafatawar hamayya tsakanin Sunderland da Newcastle a Stadium of Light ranar Asabar.
Rabon da kungiyoyin biyu su fuskanci juna tun 2016 a wasan hamayya da ake kira Tyne-Wear.
Tun daga ranar Alhamis za a fara karawar zagaye na uku tsakanin Crystal Palace da Everton.
Akwai karawa tsakanin kungiyar da ba ta buga lik, Aldershot Town da mai karawa a Championship, West Brom, yayin da Eastleigh za ta ziyarci Newport County mai buga League Two.
Wani wasa da za a yi ranar Lahadi shi ne tsakanin Liverpool, mai FA Cup takwas da za ta je Arsenal mai kofi 14.
A kuma ranar ce mai rike da kofin bara, Manchester City za ta karbi bakuncin Huddersfield Town.
Ranar Litinin kuwa kungiyar da ke buga League One, Wigan Athletic, wadda ta ci City a wasan karshe a 2013, za ta karbi bakuncin Manchester United.
Wasannin zagaye na uku a FA Cup
Ranar Alhamis 4 ga watan Janairu
- Crystal Palace da Everton
Juma'a 5 ga watan Janairu
- Brentford da Wolverhampton Wanderers
- Fulham da Rotherham United
- Tottenham da Burnley
Asabar 6 ga watan Janairu
- AFC Wimbledon da Ipswich Town
- Millwall da Leicester City
- Coventry City da Oxford United
- Maidstone United da Stevenage
- Sunderland da Newcastle United
- Stoke City da Brighton & Hove Albion
- Norwich City da Bristol Rovers
- Southampton da Walsall
- Watford da Chesterfield
- Blackburn Rovers da Cambridge United
- Gillingham da Sheffield United
- Queens Park Rangers da Bournemouth
- Plymouth Argyle da Sutton United
- Newport County da Eastleigh
- Hull City da Birmingham City
- Sheffield Wednesday da Cardiff City
- Middlesbrough da Aston Villa
- Swansea City da Morecambe
- Chelsea da Preston North End