Gane Mini Hanya: Tare da shugaban hukumar kula da almajirai ta Najeriya 23/11/2023

Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron shirin
Gane Mini Hanya: Tare da shugaban hukumar kula da almajirai ta Najeriya 23/11/2023
An wallafa

Hukumar kula da ilimin almajirai da yaran da ba sa zuwa makaranta ta ƙasar ta fara aikin mayar da yara sama da 22,000 makaranta a Abuja, babban birnin ƙasar.

Hukumar ta ce aikin wani zakaran gwaji ne, da fatan nan gaba zai karaɗe sauran sassan Najeriya.

A filinmu na Gane Mini Hanya Babban Sakataren hukumar, Dakta Muhammad Sani Idris, ya ce gwamnati ce za ta ɗauki nauyin karatun yaran daga matakin firamare har zuwa sakandire.