Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ko Arsenal za ta ci Nottingham Forest a Premier League ranar Talata?
Kungiyar Arsenal za ta ziyarci Nottingham Forest ranar Talata, domin buga wasan mako na 22 a gasar Premier League.
Kungiyoyin sun kara ranar 12 ga watan Agusta a 2023, inda Gunners ta yi nasara da ci 2-1 a Emirates.
Tun kan hutu Arsenal ta zura kwallo biyu a raga ta hannun Eddie Nketiah da kuma Bukayo Saka, saura minti takwwas a tashi wasan, Taiwo Awoniyi ya zare daya.
Kawo yanzu Arsenal tana mataki na ukun teburin Premier League da maki 43, iri daya da na Manchester City, wadda ta yi karawa 20.
Ita kuwa Nottingham Forest mai sabon koci, Nuno Espirito Santo, tana ta 16 a kan teburi da maki 20, bayan karawa 21.
Liverpool ce ta daya da maki 48, bayan wasa 21 a babbar gasar tamaula ta Ingila
Wasannin mako na 22 da za a buga a gasar Premier League:
Ranar Talata 30 ga watan Janairu
- Nottingham Forest da Arsenal
- Fulham da Everton
- Luton Town da Brighton & Hove Albion
- Crystal Palace da Sheffield United
- Aston Villa da Newcastle United
Ranar Laraba 31 ga watan Janairu
- Manchester City da Burnley
- Tottenham da Brentford
- Liverpool da Chelsea
Ranar Alhamis 1 ga watan Fabrairun 2024
- West Ham United da Bournemouth
- Wolverhampton Wanderers da Manchester United