Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda ake samun ƙaruwar buƙatar ruwan sha na alfarma a tsakanin masu kuɗi
- Marubuci, Suneth Perera
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- An wallafa
Kun taba jin wani wajen cin abinci da ake a cikin jerin abincin wajen akwai ruwan alfarma maimakon barasa, ko kuma bikin da aka nuna ma'aurata na shan ruwan alfarma a irin kofin nan da ake zuba barasa ko lemo a sha?
Shi wannan ruwa ba ruwa ne da kowa ya sani ba, ruwa ne irin na alfarma wanda gorar da ake zuba shi ma abar kallo ce ga kuma dan karen tsada.
A hada irin wannan ruwan da kowanne irin abinci kama daga abincin da aka fi sani har zuwa irin su kifi kamar dai yadda ake cin abinci a kora da barasa.
Irin wadannan ruwan na alfarma masu dan karan tsada an fi sanin su da 'Fine water', kuma ana samun su ne daga duwatsu ko kankarar da ta narke, wani lokaci ma ana samun irin wannan ruwa daga sama.
A yanzu akwai daruruwan kamfanonin irin wadannan ruwa na alfarma a fadin duniya, kuma shi wannan ruwa ba kamar sauran wadanda aka saba da su ba ne da ake sanyawa a roba ba.
Shin ko irin wannan ruwa na da ɗanɗano?
Kamar yadda barasa ke da dandano, haka akwai mutanen da aikinsu shi ne sanin dandanon kowanne ruwa da kuma rarrabe shi.
Milin Patel, ya ce " Ruwa ba wai kawai ruwa ne ba. Kowanne ruwa a fadin duniya na da nasa bambancin da kuma dandano".
Milin Patel, kwararre ne wajen sanin ruwa da dandanonsa da ke zaune a London.
Patel, ya shaida wa BBC cewa, yana kan wani kuduri na fahimtar da mutane musamman yara masu tasowa sanin nau'ikan ruwa da kuma dandanon ruwan da ake da su a duniya.
Ya ce, " Idan za ku iya tunawa a makaranta, an koya mana yadda ake samar da ruwa misali daga yadda turiri ke haduwa ya koma sama sai a samu ruwan sama, da yadda ruwan da ke diga kadan-kadan ke zama ruwan da za a iya amfani da shi bayan ya taru da dai makamantansu.To amma an manta da abu guda shi ne kan batun sinadaran da ke cikin ruwa."
Ya ci gaba da cewa," Idan ruwan sama ya sauko kasa, kasa na tsotse shi ko kuma ya shi ge cikin duwatsu daga nan sai kasar da kuma duwatsun su samar da sinarai a ruwan kamar sinadarin calcium da magnesium da potassium da kuma silica.To irin wadannan sinadaran ne ke ba wa ruwa dandano."
Ruwan da ake samu daga kankara ko kuma ruwan sama, wadan ba sa bi ta wata hanya ta kasa, yawanci suna da karancin wasu sinadarai idan aka hadasu da wadanda ake samu daga rijiya da duwatsu.
Patel, na da wuraren da ya ke samun ruwa a fadin duniya, kama daga ruwan fanfo ya mayar da shi irin ruwan alfarma da ake saye a kan fam 250 ko kuma dala 318. Bayan mutane sun sha irin ruwan alfarmar da yake samarwa, su kan yi kokari su bayyana yadda dandanon kowanne ruwa yake.
Mr Patel, ya ce," Muna bai wa mutane damar sanin cewa ruwa ba wai ba shi da dandano ba ne, idan ka fara amfani ko shan irin ruwan alfarmar da muke samarwa za ka sha mamaki."
Gasar ɗanɗana ruwa
Kungiyar da ke samar da ruwan roba na Fine Water, kan hada taro duk shekara inda ake hada dukkan masu samar da irin wannan ruwa a fadin duniya don a yi gasa a kan dandanon ruwan da ya fi dadi.
Yawancin wadanda ke halartar wannan gasa su ne wadanda ke samar da irin ruwan alfarma na roba da suka fito daga kauyuka.
Dr Michael Mascha, shi ne wanda ya kirkiri kungiyar masu samar da ruwa na alfarma, ya ce da farko ana yi wa wannan gasa ta dandana ruwa kallon kamar bata lokaci ko abin dariya ne.
Ya ce na fara sana'ar samar da ruwan alfarma shekaru 20 da suka gabata a lokacin da na daina shan barasa.
Ya ce nau'in ruwa na fine water na samar da abubuwa da dama wanda barasa ma ba za ta iya ba.
A yanzu akwai karuwar bukatar nau'in ruwan alfarma abin da Dr Mascha ke ganin cewa hakan zai sa a rage shan barasa da lemuna musamman a tsakanin matasa.
Shi irin wannan ruwan ruwa ne kamar kowanne ruwa to amma yadda ake sarrafa shi da inda ake samun shi, shi ke sanya shi ya fita daban da sauran ruwa kamar na fanfo.
Sannan kuma gashi ana sanya shi a robar alfarma ga kuma dandano mai dadi musamman ruwan da aka samu daga dutse.
Ruwa da abinci
Wasu gidajen cin abinci a kasashe kamar Spaniya da Amurka na bayar da takardar zabar abinci hadi da irin ruwan alfarmar da za ka zaba a ciki.
Dr Mascha, ya ce a wasu gidajen cin abincin idan ka zabi za ka ci kifi to akwai irin ruwan da ya dace ka sha tare da kifin, ma'ana akwai bukatar ka sha ruwan da yake da sinadarai marasa karfi saboda kifin da aka ci.
Irin wadannan ruwa na alfarma, sun yi suna sosai wajen kawar da shan barasa musamman a wuraren bukukuwa.
Abin da bai dace ba
Akwai miliyoyin mutane a fadin duniya da ke fama da karancin tsaftataccen ruwan sha, sannan wasu da dama daga cikinsu sun samu hanyar sayar da ruwan ga al'ummarsu.
A cewar Majalisar Dinkin Duniya, a 2022, mutane biliyan biyu da miliyan dari biyu na fama da rashin tsaftataccen ruwan sha ciki har da mutum miliyan 703 da ba su ma da hanyar samun ruwan.
Wasu masu suka sun ce samar da irin wadannan ruwa na alfarma ba shi da wata fa'ida saboda ba wani bambanci da ruwan da ake sha a fanfo.
Farashi ne kawai ya bambanta in ji su, su kuwa masana muhalli cewa suka yi irin wadannan ruwa na roba na bata muhalli.
Carolyn Roberts, farfesa ce a kwalejin Gresham da ke London, ta yi amanna cewa ba daidai ba ne a rinka kashe daruruwan daloli wajen siyan ruwan roba, yayin da akwai miliyoyin mutane kuma na fadi tashin samun tsaftataccen ruwan da za su sha.
Dr Mascha, ya ce ba wai ana samar da ruwan alfarma ga masu kudi ba ne, akwai irin wadanda ake samarwa da su da tsada wanda kudinsu bai wuce dala biyu ba.
Ya ce, " idan aka yi la'akari da hanyar da ake bi wajen hada irin wannan ruwa za a ga cewa akwai wahala ga kuma bata muhalli, don haka me ya sa ba za a inganta ruwan fanfon da ake samu ba?"
Dr Mascha, ya ce muna manta cewa samun ruwan fanfo a sha ma, dama ce saboda akwai miliyoyin mutane a fadin duniya da ba sa ma ganin ruwan fanfon.