Jorge Vilda: 'Yan wasan tawagar mata ta Spain sun nemi a korin kocinsu

An wallafa

Hukumar kwallon Sifaniya ta ce 'yan wasa 15 sun ce za su yi murabus daga bugawa tawagar kasar ta mata wasa idan ba a kori kocin kungiyar ba Jorge Vilda.

Hukumar ta ce yan wasan sun yi ikirarin cewa aiki da su na shafar tunaninsu da kuma lafiyarsu.

Amma ta ce ba abu ba ne mai yiwuwa "a bai wa yan wasa damar kalubalantar kocin kasar ba".

"Wannan irin makanisar abu ne da za ka iya kama misali da shi a fannin kwallon kafa da wasanni," in ji su.

"Daukar wannan matakin ba a hannunsu yake ba."

Ta yi gargadin cewa kin bugawa tawagar kasa wasa "gagarumin laifi ne da zai iya janyowa dan wasa hukuncin daurin shekara biyu da kuma dakatar da shi daga buga wasa na tsawon shekara biyar".

"Aikin hukumar shi ne hada kan yan wasa ko da kuwa da yara za su yi wasa," in ji ta.

"Wannan lamari ya wuce maganar wasanni ya shiga maganar kima. Ba za mu bayar da kai ba a wajen zabe. Wani abu ne da ba mu taba hasashe ba a tarihin kwallon kafa, a bangare kwallon kafar mata da mza a Sifaniya da ma duniya baki daya.

"Tawagar kasar na bukatar yan wasan su mayar da hankali kan wasanni, sanye da rigar kasar mu abar alfaharinmu."

Vilda mai shekara 41, shi ne kocin kasar tun 2015 kuma yakai kasar wasan kusa da daf da na karshe a gasar Euro 22, wanda daga baya Ingila ta lashe kofin.

A 2015 Vilda ya gaji Ignacio Quereda, wanda ya ajiye aikinsa bayan 'yan wasan sun nemi da ya yi murabus.

Hakan ya faru ne bayan da Sifaniyan ta kare a mataki na karshe a rukunin da suke a gasar cin kofin duniya.