Mata masu kokawa da mawaƙin Fulu Miziki cikin hotunan Afirka

An wallafa

Zaɓaɓɓun ƙayatattun hotunan Afirka na da ƴan nahiyar daga wasu sassan duniya daban-daban

Ɗaya daga cikin mawaƙan ƙungiyar Fulu Miziki a lokacin da yake shirin yin wasa a dandalin bikin kaɗe-kaɗe da waƙe-waƙe na Glastonbury a ranar Alhamis.

Mata biyu ƴan wasan kokowa da suka yi ragas a wasan kokowa na bakin teku a babban birnin Senegal Dakar a ranar Lahadi.

Mutane sun gudanar da tattakin São João Baptista a Cape Verde duk da zafin rana da ake yi.

...An yi ta buga ganga a lokacin da ake tattakin na tsawon kilomita 23...

...yadda suka riƙa rawa a yayin tattakin.....

Ɗan wasan Cricket na Afirka ta Kudu Tabraiz Shamsi na murnar nasarar da ƙungiyarsa ta samu a kan Afghanistan, inda ta kai wasan ƙarshe na gasar cin kofin duniya ta T20 a karon farko.

Yadda aka samu hargitsi tsakanin ƴansanda da masu zanga-zangar nuna adawa da sabuwar dokar hada-hadar kuɗi da shugaban Kenya ya gabatar, da ta ƙunshi ƙarin haraji, a Nairobi babban birnin ƙasar Kenya.

A lokacin da wani mutum ke kallon bayanin shugaba Ruto ga ƴan ƙasar, inda ya ce ya janye ƙudurin dokar saboda zanga-zangar da aka yi a ƙasar.

Wani mutum na zagayawa a cikin kasuwar Raƙuma ta Nouakchott, babban birnin Mauritania a ranar Laraba gabanin zaɓen shugaban ƙasar.

A ranar Alhamis, ɗan wasan rawar laƙwasa jiki Mohamed Chakib, ɗan asalin Algeria ya fafata a wasan share fage na Olumpic wanda zai ba shi damar zuwa wasan Olumpics na 2024 da za a yi a birnin Paris.