Ƴar Najeriyar da aka kashe mijinta a Italiya na son a mata adalci

An wallafa

Matar wani ɗan Najeriya mai sayar da kaya a titi da aka kashe a Italiya ta gaya wa BBC cewa tana neman a yi mata adalci a kan mutuwar mijin nata da ta yi mata tsannain ciwo.

Aliku Ogorchukwu, ɗan shekara 39 yana sayar da da hankici ne agarin Civitanova Marche da ke gaɓar tekun a ranar Juma'ar da ta wuce, a lokacin da aka bi shi aka yi masa duka har ya mutu.

An kama wani dan Italiya mai shekara 32 a kan zargin kisa da sata. Wani bidiyo da ya yi ta yawo a shafukan sada zumunta ya nuna mutumin a kan Ogorchukwu, yana naushin sa da hannu.

Babu wanda ya yi ƙoƙarin ceton sa cikin waɗanda suka shaida lamarin da ya farun a ido na ganin ido.

"Wannan wata irin mugunta ce da ban san irinta ba", matar Ogorchukwu, Charity Oriachi, ta gaya wa BBC Afirka.

Ms Oriachi ta ce ta samu taimako kan bayanin yadda mijin nata ya mutu amma ta gaji da yin "magana".

Yanzu abun da kawai take so shine a bi mata hakkinta, ta ce ƴan uwanta sun daɗe suna zama a Italiya, kuma mijinta bai taɓa zuwa neman faɗa ba.

Kisan ya haifar da ɓacin rai a cikin al'ummar yankin, da ƴan Najeriya da suka fara zanga-zanga kuma suna shirya yin wata nan ba da daɗewa ba.

Gwamnatin Najeriya ta ce wa hukumomin Italiya su gaggauta gurfanar da wanda ya aikata wannan ɗanyen aiki a gaban ƙuliya.

Ba a ba da belin wanda ake zargi ba

An bayar da umarnin ci gaba da tsare wanda ake zargin, mai suna Filippo Claudio Giuseppe Ferlazzo, har sai an kammala bincike.

Lauyan da ke kare shi ya shaida wa manema labarai cewa wanda ake zargin ya bayar da haƙuri kuma babu wani ƙabilanci cikin abin da ya haɗa su ɗin.

Wani dan sanda mai binciken ya ce an kai wa Ogorchukwu hari ne bayan da dan kasuwar ya nace sai wanda ake tuhuma da abudurwarsa sun bar masa canji.

Budurwar mai suna Elena D, ya shaida wa Italiya Corriere della Sera cewa Ogorchukwu ya taɓa hannunta, amma hakan bai dame ta ba.

Ms Oriachi now wants to see the suspect "face to face", to understand why he killed her husband, the family's lawyer told the Associated Press.

A yanzu Ms Oriachi tana son ganin wanda ake zargin ido da ido don fahimtar dalilin da ya sa ya kashe mijinta, kamar yadda lauyansu ya shaida wa kamfanin labarai na Associated Press.