Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Yan Brazil ''ba za su daina rawa ba'' idan sun ci kwallo
Kociyan Brazil, Tite ya ce ba zai nemi afuwa ga duk wadanda ba sa jin dadi da rawar da 'yan wasansa ke yi idan sun ci kwallo a Gasar Cin Kofin Duniya a Qatar.
Shi kansa kocin ya yi rawa a wasan da Brazil ta casa Koriya ta Kudu da ci 4-1 a wasan zagaye na biyu ranar Talata.
''Yadda na shaku da 'yan wasan kenan kuma matasa - za su iya zama ma jikokina ne,'' in ji kociyan.
''Idan har sai na yi rawa zan samu shakuwa da su zan ci gaba da tikar rawar.''
A hira da aka yi da shi kan wasa da Croatia a quarter finals ranar Juma'a kociyan ce: ''Ba zan bayar da hakuri ba, bayan da dabi'armu ce rawa da annashuwa.''
Dan wasan Brazil, Vinicius Junior da Neymar sune ke jan ragamr tikar rawa, bayan cin Koriya ta Kudu kwallayen.
Richarlison shi kuwa zuwa wajen koci Tite ya yi suka ci gaba da rawa tare lokacin da Brazil ta zura na uku a raga.
Tsohon dan kwallon Jamhuriyar Ireland, Roy Keane bai goyi bayan rawar da 'yan wasan Brazil ke yi, inda ya ce rashin ''martaba'' ce ga Koriya.
Tite ya yi watsi da batun da cewar yana da alhakin bunkasa al'adar Brazil a fannin kwallon kafa a duniya.