Inter na gogayya da Liverpool kan Kimmich, Guardiola zai yanke shawara kan Grealish

Joshua Kimmich

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Inter Milan na shirin hamayya da Liverpool wurin rige-rigen ɗaukar ɗan wasan tsakiyar Jamus Joshua Kimmich, a daidai lokacin da ɗan wasan mai shekaru 30 ya shiga watannin ƙarshe na kwantiraginsa da Bayern Munich. (Teamtalk)

Kocin Manchester City Pep Guardiola na shirin yanke shawara kan makomar ɗan wasan gaban Ingila Jack Grealish, mai shekara 29, yayin da ake shirin yi wa tawagar ƴan wasan kulob ɗin garambawul.(Football Insider)

Real Madrid na sanya ido kan ɗan wasan tsakiya na Ingila Adam Wharton bayan da ɗan wasan mai shekaru 21 ya koma taka leda a Crystal Palace. (Mail)

Manchester United da Tottenham da Arsenal sun nuna sha'awarsu ta ɗaukar Benjamin Sesko daga RB Leipzig, kuma ɗan wasan na Slovenia mai shekara 21 yana iya tafiya a wannan bazarar, kan farashin da zai kai Yuro miliyan 80 (£66m). (Sky Sport Germany)

Fulham da Sporting suna zawarcin ɗan wasan baya na ƙasar Girka Georgios Vagiannidis daga Panathinaikos inda Sporting ta riga ta miƙa tayin Yuro miliyan 10 (£8.3m) kan ɗan wasan mai shekara 23. (Football Insider)

Ɗan wasan gaban ƙasar Canada Jonathan David ya ki amincewa da buƙatar Lille ta tsawaita kwantiraginsa, yayin da ɗan wasan mai shekara 25 ya shirya barin ƙungiyar a matsayin ɗan wasa mai zaman kansa a ƙarshen kakar wasan bana. (Nicolo Schira)

Liverpool ta fara tattaunawa da Conor Bradley kan sabon kwantiragi na tsawon shekaru biyar, inda ɗan wasan bayan na Ireland ta arewa, mai shekara 21, zai samu ƙarin albashin kashi 650 cikin 100. (Sun)

Ɗan wasan baya na Jamus Jonathan Tah, mai shekara 29, zai bar Bayer Leverkusen a matsayin ɗan wasa mai zaman kansa a ƙarshen kakar wasa ta bana. (Nicolo Schira)

An samu ci gaba a tattaunawar da ake yi tsakanin Leroy Sane da Bayern Munich kan sabon kwantiragin ɗan wasan na Jamus, mai shekara 29. (Sky Sport Germany)

Ana kyautata zaton tsohon darektan wasannin Atletico Madrid Andrea Berta yana cikin jerin masu neman maye gurbin Edu a matsayin darektan wasanni na Arsenal. (Telegraph)

Brentford da Fulham sun nuna sha'awarsu ta ɗaukar ɗan wasan bayan Mexico Johan Vasquez, mai shekara 26, daga Genoa. (GiveMeSport)

Chelsea tana harin Golan Brighton ɗan ƙasar Netherlands Bart Verbruggen, mai shekara 22, inda ta ke shirin ɗaukarsa a bazara mai zuwa. (GiveMeSport)