Waiwaye: An fara kamfe a hukumance, 'yan majalisa za su ga Buhari kan yajin aikin ASUU

Waiwaye: An fara kamfe a hukumance, 'yan majalisa za su ga Buhari kan yajin aikin ASUU

Daga cikin abubuwan da suka faru a makon da ya gabata a Najeriya har da fara kamfe na zaɓen 2023, da martanin fadar shugaban ƙasa kan sayen bindigogi da ake zargin wasu jihohi na yi.

A wannan maƙalar, mun duba wasu daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a makon.

Babu jihar Najeriya da ke da izinin sayo makamai kamar AK-47 - Fadar Shugaban Ƙasa

Fadar Shugaban Najeriya ta fitar da wata sanarwa da ke cewa babu wata jihar kasar da aka ba izinin sayo makaman yaki masu sarrafa kansu domin raba wa kungiyoyinsu na samar da tsaro.

Sanarwar Fadar ta kuma ce ta dade tana nanata cewa babu mutumin da aka ba izinin mallakar bindiga iri samfurin AK-47 ko ma wata bindiga mai sarrafa kanta, inda ta ce tilas ne su mika irin bindigogin ga hukumomin tsaron kasar.

Fadar ta kuma ce an ba jami'an tsaro umarni su hukunta wadanda suka ki bin wannan umarnin.

Mallam Garba Shehu, wanda shi ne mai magana da yawun Shugaba Muhammadu Buhari ne ya sanya hannu kan wannan sanarwar.

Ya tabo batun Jihar Katsina, wadda ya ce gwamnan jihar ya rubuta wasikar yana bayyana ceaa ya gayyaci shugaban kwalejin da ke horar da jami'an Civil Defence da ya tura nasa jami'an Katsina domin su koyar da 'yan bijilanten jihar yadda ake amfani da bindiga amma ba mai sarrafa kanta ba.

Sanarwar ta kuma yi kira ga jama'ar kasar da su guji mayar da batun tsaro ya koma tamkar na siyasa.

Zaben 2023: 'Yan takara sun sa hannu a kan zaman lafiya

'Yan takarar shugaban kasa a zaben 2023 na Najeriya sun sa hannu kan yarjejeniyar tabbatar da zaman lafiya a birnin Abuja.

An ga fuskokin 'yan takara kamar na jam'iyyar Labour, Peter Obi da mataimakin dan takarar jam'iyyar APC Kashim Shettima da Atiku Abubakar, dan takarar babbar jam'iyyar adawa ta Najeriya.

Karin 'yan takarar sun hadar da na jam'iyyar NNPP, Rabi'u Musa Kwankwaso da Hamza Al-Mustafa na jam'iyyar AA, akwai Omoyele Sowore na jam'iyyar AAC.

Kwamitin tabbatar da zaman lafiya a lokacin zaben Najeriya karkashin jagorancin Janar Abdulsalami Abubakar (mai ritaya) ne ya shirya wannan taro don sa hannu a kan yarjejeniyar

Atiku ya ƙaddamar da tawagar kamfe ɗinsa

Bayan shafe tsawon lokaci ana hanƙoron zuwan wannan rana, jam'iyyun siyasa a Najeriya sun fara yawon neman ƙuri'un masu zaɓe a hukumance.

Babbar jam'iyyar adawa ta PDP ba ta yi ƙasa a gwiwa ba, inda ta ƙaddamar da tawagar kamfe ɗinta na takarar shugaban ƙasa a ɗakin taro na International Conference Centre da ke Abuja ranar Laraba.

Ɗan takarar tata Atiku Abubakar da ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa, Ifeanyi Okowa, da sauran jiga-jigai na cikin waɗanda suka yi jawabai a wurin taron."

Akasarin mutanen da suka taru a nan ƙwararrun 'yan siyasa ne irina waɗanda siyasa ke gudana a cikin jininsu saboda ƙaunar da suke yi wa mutane da kuma ƙasarsu," in ji Atiku.

Duk da cewa babban abin da ya tara su shi ne ƙaddamar da tawagar kamfe, an kuma ƙaddamar da wani littafi da aka rubuta game da hukunce-hukuncen da kotuna suka bayar game da ƙararrakin da Atiku ya shigar a tsawon shekaru mai suna 'Landmark Constitutional Law Cases in Nigeria; The Atiku Abubakar Cases'.

Shugabannin majalisa za su gana da Buhari kan yajin aikin ASUU

Shugabannin Majalisar Wakilan Najeriya za su gana da Shugaba Muhammadu Buhari game da batun yajin aikin malaman jami'a ƙarƙashin ƙungiyar ASUU, wanda suka shafe wata kusan bakwai suna yi.

Wata sanarwa ta ce Kakakin Majalisa Femi Gbajabeamila ya ce nan da 'yan kwanaki za su fitar da rahoton tattaunawar da suka yi da shugabancin ASUU da zimmar bai wa Buhari "don ya samu wasu bayanai na daban" don ɗaukar matakin da ya dace.

Lamarin na zuwa ne yayin da ofishin ministan shari'a ya ce zai duba ƙorafin ASUU kan batun tsarin biyan albashi na IPPIS da kuma UTAS, wanda shi ne babban batun da ya jawo yajin aikin.

A yau Alhamis ne shugabannin majalisar suka gana da ASUU, inda ministan ƙwadago da shugabar ma'aikatan gwamnatin tarayya da sakataren gwamnati suka halarta da zimmar kawo ƙarshen yajin aikin.

"Za mu rubuta matsayarmu da shawarwarinmu mu kai wa shugaban ƙasa, abin da ya sa muka taru ke nan don neman mafita," a cewar Mista Gbajabeamila.

Ahmed Lawan ya karbi kaddara kan hukuncin kotun da ya soke takararsa

Shugaban Majalisar Dattijai Sanata Ahmed Lawan ya ce ya karbi hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ya ce ba shi ne halattaccen dan takarar majalisar dattijai na jam'iyyar APC a mazabar Yobe ta Arewa ba.

Matakin na zuwa ne kwana guda bayan hukuncin kotun da ke zamanta a birnin Damaturu game da halattaccen dan takarar sanata a jam'iyyar APC daga mazabar Yobe ta Arewa.

Cikin sanarwar da ya wallafa a shafinsa nasada zumunta, Sanata Ahmed Lawan ya ce bayan tuntubar abokan harkar siyasa da magoya baya da abokan arziki, "Na yanke shawara ba zan daukaka kara a kan hukuncin ba. Na karbi kaddara".

Sanarwar ta kunshi wani bayani mai alamta yin ban kwana, inda ya yi godiya ga shugabannin siyasar jiharsa ta Yobe da ma al'ummar mazabarsa da ya wakilta tsawon shekaru a majalisun tarayyar Najeriya.

Mikel Obi ya yi ritaya daga wasan kwallon kafa
An wallafa

Tsohon kyaftin din kungiyar kwallon kafa na Najeriya Mikel John Obi ya sanar da ritayarsa daga wasan kwallon kafa.

Mikel Obi ya sanar da matakin ne ranar Talata a shafinsa na Instagram.

Ya lashe gasar Zakarun Turai a 2012 tare da tsohuwar kungiyarsa ta Chelsea, baya ga wasu jerin kofunan da ya lashe, kuma a baya-bayan nan yana buga wa kungiyar Kuwait SC ne.

Ga wani abu cikin sakon da ya wallafa a Instagram:

"Akwai wani karin magana da ke cewa komai na da karshe kuma haka lamarin yake ga wasan kwallon da na dade ina bugawa. Yau ita ce ranar da wasan kwallo ya zo karshe a rayuwata".

Arewa maso yammacin Najeriya na fama da gagarumar matsalar kiwon lafiya - MSF

Kungiyar likitocin duniya ta Medecins Sans Frontieres (MSF) ta ce arewa maso yammacin Najeriya na fuskantar gagarumar matsalar kiwon lafiya.

Kungiyar ta ce kananan yara masu dimbin yawa suna fuskantar matsalar tamoiwa.

MSF ta bayar da kulawa ga kananan yara 100,000 da ke fama da tamowa tun daga farkon shekarar nan, tana mai cewa kimanin yara 17,000 suna bukatar kulawar asibiti.

Kungiyar ta kara da cewa taimakon da ake bai wa yaran ya yi matukar kadan, domin kuwa an mayar da hankali kan yankin arewa maso gabashin kasar inda ake fama da rikicin Boko Haram.