Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Daga fitilar keke na gano yadda ake sarrafa iska zuwa lantarki'
'Daga fitilar keke na gano yadda ake sarrafa iska zuwa lantarki'
An wallafa
Jamilu Muhammad Injiniya ne a jihar Kaduna da ya shafe fiye da shekara 30 yana harhaɗawa da gyaran kayayyaki masu amfani da lantarki.
Babban aikinsa a yanzu shi ne samar da wutar lantarki daga iska - wato wind turbine a Ingilishi.
Ya faɗa wa BBC cewa ya gano yadda ake sarrafa fankokin da za su ba da lantarki ne bayan ya nazarci fitilar keke irin na da da ke haskawa idan mutum yana tuƙawa.
Yanzu haka yana da mutum aƙalla 15 da ke aiki a ƙarƙashinsa.