Madrid ta Cimma yarjejeniya da Modric, Bayern na nazarin daukar De Zerbi

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid ta cimma yarjejeniya da Luka Modric na tsawaita kwantiragin dan wasan tsakiyan na Croatia mai shekara 38 na karin shekara daya. (Onda Madrid, via Mundo Deportivo, in Spanish)
Kocin Brighton Roberto de Zerbi, mai shekara 44 ne kan gaba a jerin sunayen da Bayern Munich ke nema don maye gurbin Thomas Tuchel a matsayin kocinta a bazara. (Bild, in German)
Bayern ta shaida wa wakilan De Zerbi cewa a shirye ta ke ta biya Brighton fam miliyan 12. Dan Italiyan ya yanke shawarar kin kabar aikin AC Milan, amma yana sha'awar kungiyar ta Jamus. (HITC)
Newcastle United na son ta dauko golan Arsenal da Ingila Aaron Ramsdale kuma a shirye suke su biya fam miliyan 15 kan dan wasan mai shekaru 26. (Telegraph)
Crystal Palace da Fulham duk suna duba yiwuwar sayen dan wasan tsakiya na Fiorentina da Morocco, Sofyan Amrabat, mai shekara 27, wanda ke zaman aro a Manchester United. (Sun)
Manchester United na da damar daukar Massimiliano Allegri wanda ta dade tana zawarci a matsayin kocinta bayan Juventus ta sallami dan kasar Italiyan mai shekara 56. (Express)
Akwai yiwuwar Manchester United za ta karawa dan wasan tsakiyar Portugal Bruno Fernandes, mai shekara 29, albashi daga kwantiraginsa na fam 230,000 a duk mako domin ta ci gaba da rike kyaftin din nata. (Star)
United za ta yi watsi da duk wani tayi kan Fernandes a wannan bazarar saboda ba ta da niyyar sayar da dan wasan tsakiyan (Caught Offside)
Chelsea na ganin ta yi nasarar sayen dan wasan Brazil Estevao Willian mai shekara 17 bayan ta amince da yarjejeniyar da ta kai fam miliyan 60 da Palmeiras. (HITC)
AC Milan ta sake tuntubar kocin Lille Paulo Fonseca. Dan kasar Portugal mai shekara 51, yana son maye gurbin Stefano Pioli a San Siro. (Fabrizio Romano)
Manchester United na son a rage mata farashi kan Jarrad Branthwaite bayan da ta yanke shawarar ba za ta biya Everton fam miliyan 80 kan wasan bayan na Ingila mai shekara 21 ba. (Givemesport)
Wolves na shirin daukar dan wasan gaban Southampton da Scotland Che Adams, mai shekara 27, kan cinikin kyauta duk da Everton da Leeds United suma suna zawarcinsa. (Talk)









