Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Broja na Chelsea ya ji rauni a wasan sada zumunta da Aston Villa
Kociyan Chelsea, Graham Potter ya ce raunin da Armando Broja ya ji a wasan sada zumunta da Aston Villa zai iya zama mai muni ga dan kwallon.
Dan wasan tawagar Albania, mai shekara 21 ya yi karo da mai tsaron baya, Ezri Konsa a wasan da suka buga a Abu Dhabi.
Nan da nan dan wasan ya rike gwiwar kafarsa yana ta kuwa, hakan na nufin ya bugu sosai, inda aka fitar da shi daga fili a kan gadon daukar mara lafiya.
''Zai yi wuri a fayyace girman raunin da ya ji a wannan lokacin, amma dai da alama abin ya yi muni.'' in ji Potter.
Broja ya yi wa Chelsea karawa 12 a Premier League a kakar nan, 10 daga ciki sauyin dan wasa ya yi da cin kwallo daya.
A kakar da ta wuce dan kwallon ya yi wasannin aro a Southampton.
Chelsea wadda ta yi rashin nasara a wasa uku a jere kan fara Gasar Kofin Duniya za ta fafata da Bournemouth a Stanford Bridge ranar 27 ga watan Disamba.
Za a koma wasannin Premier League bayan Kirsimeti, idan an kammala Gasar Kofin Duniya ranar 18 ga watan Disamba.
Chelsea tana ta takwas a teburin Premier League, bayan da Arsenal ce kan gaba.