Yadda aka ceto rayuwata ta hanyar mayar da ni Ghana da karatu daga London

    • Marubuci, Mark Wilberforce
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Accra
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 7

A lokacin da mahaifiyata ta shaida min cewa za mu je hutu Ghana daga London, ban yi wani shakku ba, lokacin ina ɗan shekara 16 a duniya.

A tunanina za mu je gajeren hutu ne mu dawo, saboda haka ba wani abin damuwa ba ne.

Bayan mun yi wata ɗaya a Ghana ne mahaifiyata ke sanar da ni cewa ba zan sake komawa London ba har sai na shiryu na kuma tara kudi masu yawan da zan iya ci gaba da karatu da su.

Ni ma an yi min balulluɓa irin wadda aka yi wa matashin da kwananan ya maka iyayensa ƙara a babbar kotu da ke London kan tura shi karatu Ghana da suka yi.

A yayin da iyayen matashin ke ƙoƙarin kare kansu sun ce sun aikata haka ne saboda ba su son a kashe masu shi ta hanyar caka mashi wuƙa a bisa titunan London.

A lokacin a tsakiyar 1990 mahaifiyata wadda malamar makarantar firamare ce, ta aikata hakan ne saboda irin wannan damuwa.

A lokacin sau biyu ana kora ta daga makarantar sakandire, inda na koma yawon gararanba da abokan banza da muke cikin hatsari koda yaushe.

Manyan abokaina da muka fi kusanci da su daga karshe kama su aka yi da laifin fashi da makami. In da na ci gaba da zama a London da tare za a yanke mana hukunci.

Sai dai mayar da ni Ghana shi ma kusan daidai yake da tura ni gidan yari.

Na tausaya wa matashin nan da ya ce ji yake kamar an saka shi cikin wuta.

A lokacin da na cika shekara 21 na fahimci cewa matakin da mahaifiyata ta dauka shi ne yafi dacewa da rayuwata.

Ban je makarantar kwana kamar yadda wancan matashi ya yi ba, mahaifiyata ta sanya ni makarantar je ka ka dawo karkashin kulawar yan'uwanta maza.

Da farko na zauna da kawuna Fiifi, tsohon mai kula da muhalli na Majalisar Dinkin Duniya, a wani gari, Dansoman da ke kusa da babban birnin Ghana, Accra.

Na sha wahala saboda sauyin rayuwa, a London ina da ɗakina na daban da abin wanki, akwai ƴanci sosai, zan yi duk abin da nake so.

A Ghana ina tashi karfe 05:00 na asuba domin share harabar gida da wanke motocin kawuna da matarsa.

Wata rana na saci motar ta ga shi ban iya tuki ba, haka na je na fada ma motar wani babban soja.

Na yi yunkurin guduwa, sai dai sojan ya kamata ni ya kuma yi mani barazanar kai ni sansanin Burma, sansanin soji mafi hatsari da a baya mutane ke zuwa ba tare da sun dawo ba.

Wannan shi ne abu na karshe marar kyau da na aikata.

Ba hora ni kadai aka yi a Ghana ba, a'a har hangen nesa sai da na koya.

Rayuwa a Ghana na gane cewa akwai wasu abubuwan da nake dauka da rashin mahimmanci, alhali ni'ima ce babba a gare ni. Misali wanke kaya da hannuna da shirya abinci.

Wani lokacin sai in ji kamar ana azabtar da ni, sai dai daga bisani sai na fahimci ana koya mani sanin rayuwa da jajircewa ne.

Da farko kawuna ya yi tunanin sanya ni daya daga cikin manyan makarantun masu kudi na Ghana, sai dai daga bisani saboda hangen nesansu da tsoron kada in kara kafa wata kungiyar marasa jin magana, sai suka sanya ni makarantar gwamnati inda mahaifina ya yi.

Ana koyarwa a cikin aji da turanci, sai dai a wajen makaranta ana magana ne da yaruka kala-kala, wadanda ban sha wahala wajen koyon su ba.

A London ina kokarin koyon yadda ake magana da yaren mahaifiyata na Fante, sai dai ban kware ba.

A lokacin da na koma birnin Tema domin ci gaba da zama da kawuna da na fi so, kawu Jojo, wanda yake kwararre a harkar noma, an mayar da ni a babbar makarantar sakandare ta Tema.

Sabanin abin da yaron nan da ya karade manyan jaridu a Birtaniya ya fada, cewa tsarin ilimin Ghana bai kai inda ake so ba.

A Birtnaiya ana mani kallon mai kaifin basira sosai, duk da rashin jin maganata, amman da na zo Ghana na sha wahala saboda dalibai yan shekaruna suna da kokari sosai musamman bangaren lissafi da kimiyya.

Tsarin karatun Ghana ya sanya na dage sosai fiye da yadda na yi a London.

Bayan samun nasara a bangaren karatuna, mutanen Ghana sun koya mani dabi'u masu kyau da zan ci gaba da rayuwa da su har karshen rayuwata.

Akwai batun girmama manya, inda na yi rayuwa ana gaida dukkan wanda ya girme maka.

Bayan ɗa'a da ladabi da na koya a Ghana na kuma koyi rashin tsoro da jajircewa.

Kwallon kafa ta taka muhimmiyar rawa wajen sauya ni. Na rika buga kwallo a wani wajen shakatawa da ke cike da duwatsu da jar kasa da buraguzai sabanin inda na baro a Birtaniya da komai tsaf-tsaf.

Hakan ya sanya na fahimci shi ya sa yawancin wadanda suke taka leda kwararru a Birtaniya sun fito ne daga Afirka ta Yamma.

A Ghana ba wai iyawa kadai ake koyo ba, a'a har da jajircewa da hakuri, da fadi tashi da ba su hana mutum ya ci gaba da jajircewa.

Duk ranar Lahadi, ina buga kwallo a bakin teku, sai dai nakan je a makare saboda kawuna ba ya bari na gida, tare muke zuwa coci.

Ina jin kamar wadannan abubuwan za su ci gaba da tafiya a haka har abada, sai dai ina da yakinin cewa Ghana kasa ce da ke cike da masu tsoron Allah.

Watanni 18 na farkon rayuwata a Ghana su ne mafiya tsauri, saboda a cikinsu ne na san a hanani in hanu da kuma koyon aikin gida da ladabi da ɗa'a.

Na yi yunƙurin sace fasfo dina in gudu zuwa London, sai dai mahaifiyata ta sha gabana ta yi masa boyen kwarai, babu hanyar da zan bi in gudu.

Zaɓin da ya rage mani shi ne in tsaya in saba da rayuwarsu, inda daga bisani na daina kallon Ghana a matsayin gidan yari, na fara mata kallon wuri mai cike da farin ciki da walwala.

Na san wasu irina da dama da aka mayar Ghana wadanda iyayensu ke rayuwa a London.

Michael Adom yana shekara 17 aka mayar da shi Accra a 1990, ya bayyana rayuwarsa a Ghana a matsayin marar dadi, inda ya koma London bayan ya cika shekara 23 yanzu haka yana aiki a matsayin jam'in gwaji.

Abin da ya fi korafi a kai shi shi ne kaɗaici, ya ce ya yi kewar yan gidansu da abokansa.

Ya yi korafin ba ya gane me ake cewa shi ma ba a fahimtarsa saboda iyayensu ba su koya mashi da yan'uwanshi yarensu ba.

Hakan ne ya sanya ya sha wahala sosai a shekaru biyu da rabi na zamansa Ghana.

Idan ya je sayen kaya ana cika masa kudi saboda ana kallon shi a matsayin bako, "Duk inda zan je sai na tafi da wani."

Amma daga bisani ya zo ya kware da yaren Twi , ya kuma yi amannar hakan ci gaba ne a gare shi.

"Zamana a Ghana ya sanya na san ciwon kaina, ya kuma taimaka min wajen sanin ko ni waye, a matsayina na dan Ghana na fahimci al'aduna da tarihin asalina."

A shekara ta uku, na kamu da son al'adunmu na Ghana, inda hakan ya sanya na kara kusan shekara biyu bayan kammala karatuna na Sakandire.

Na rika yabawa da abincin Ghana saboda ban taba tunanin a lokacin da nake London zan iya cin abin da nake ci a Ghana ba, kowane abinci yana da nashi tarihin, ba kamar a London ba.

Na kamu da kaunar 'Waakye' wani abinci da ake yi da shinkafa, da ake dafawa da ganyen gero, da ke bashi wani launin shudi ana yawanci cin shi da soyayyen Ayaba, wato plaintain.

Ina jin dadin wakokin Ghana, ina kuma kaunar mutanen Ghana, yanzu kam ba na ji na a matsayin wanda aka tsare, face wanda ke jin dadin rayuwa a Ghana.

Bayan rasuwar mahaifiyata, Patience Wilberforce, kwanan nan na kara fahimtar dalilinta na mayar da ni Ghana.

Ta ceci rayuwata, ta tseratar da ni daga aikata manyan laifuka.

Na koma London na ci gaba da karatu a College of North West London, a lokacin da na cika shekara 20, inda na karanta harkar da ta shafi aikin jarida daga bisani na soma aiki da gidan radio na BBC Radio 1Xtra.

Wani da muke tare a kwaleji bai samu irin damar da na samu ba.

Zamana a Ghana ya sauya mani tunani kan makomata da dabi'una, na zama cikakken mutum.

Saboda haka har abada zan kasance mai biyayya ga mahifiyata da kawuna da kuma kasata da ta cece ni.

Mark Wilberforce dan jaridar wucin gadi ne da ke zaune a London da Accra.