Lafiya Zinariya: Me ya sa mata suka fi rashin rike fitsari?
Lafiya Zinariya: Me ya sa mata suka fi rashin rike fitsari?
An wallafa
Mata sun fi maza samun matsalar rashin rikon fitsari saboda yawan haihuwa, a cewar masana.
Likitoci sun bayyana cewa matsalar ta rabu kashi-kashi, kuma sai an je asibiti sannan ake tantance wanda ke damun mace.
Matsalar na sanya mata jin kunya da rashin walwala da takura a rayuwarsu.
Sai dai a cewar likitoci matsala ce da ke da magani, saboda haka akwai buƙatar masu matsalar su je asibiti domin samun maganin da ya dace.
Manyan rabe-raben matsalar rashin rikon fitsarin sun haɗa da:
- Matsuwa(Urgency): Mafitsara bata iya ɗaukar fitsari da yawa, saboda bata aiki sosai.
- Takura (Stress): Bututu ko kofar mafitsara na da matsala, don haka duk wani yunƙuri zai sa fitsari ya zubo. Kamar lokacin atishawa, tari da makamantansu. Matan da suka haihu ko masu ciki sun fi samun wannan.
- Tumbatsa (Over flow): Jijiyoyin da ke jikin mafitsara da ke aikawa da saƙo na da matsala, ta yadda saƙon baya isa ƙwaƙwalwa. Masu ciwon suga da bugun jini sun fi fuskantar wannan.
- Gaza zuwa inda za a yi fitsarin: Saboda wasu matsaloli kamar na rashin lafiya, kamar masu zama a keken guragu. A nan mafitsarar bata da wata matsala, amma mutum ba zai iya zuwa banɗaki ko inda ya kama ba ya yi fitsarin.
Domin jin abubuwan da ke janyo wannan matsalar da matakan magance ta, Dr. Ruƙayya Muhammad Babandi ta yi cikakken bayani.
Latsa makunni na sama domin sauraron shirin.