Yadda jami'a ta kori ɗalibai bisa zargin auren jinsi a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar gudanarwar jami'ar kimiyya da fasaha ta Confluence University of Science and Technology (CUSTECH) da ke garin Osara na jihar Kogi a Arewa ta tsakiyar Najeriya ta amince da korar wasu ɗalibai biyu da ake zargi da neman jinsi.
Hukumar jami'ar ta kuma dakatar da wasu ɗaliban huɗu na tsawon shekara ɗaya saboda kama su da laifin yin faɗa a cikin harabar makarantar.
Sanarwar da hukumar gudanarwar jami'ar ta fitar a ranar Juma'a 24 ga watan Ogusta ta ce an ɗauki matakin ne bayan babban taron kwamitin gudanarwar jami'ar karo na 31 ya amince da rahoton kwamitin ɗa'ar ɗalibai kan batun.
Mataimakin magatakardar jami'ar, Eli Gbadafu a cikin wasiƙar da ya aikewa ɗaliban da abin ya shafa ya ce makarantar ta ɗauki matakin ne a bisa dokar rayuwar ɗalibai a makarantar ta 2025 da aka yi wa gyara.
Jami'ar ta ce ɗaliban da aka kora sun haɗa da mai karatun digiri kan koyarwa mai neman ƙwarewa kan ilimin halitta (Biology) da kuma mai karatun digiri a fannin haƙar ma'adinar (Mining Engineering)
Sauran ɗaliban da aka dakatar saboda kama su suna faɗa a harabar makarantar kuma mata ne.
Hukumar makarantar ta ti gargaɗin cewa ba zata sassauta ba wajen zartar da hukunci kan duk wani ɗalibi da aka kama da karya dokar jami'ar.
"Don haka muna shawartar ɗalibai su nazarci wannan littafi na kundin dokokin jami'ar kuma su gudanar da rayuwa bisa tanadin doka,'' in ji sanarwar jami'ar.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Najeriya na cikin ƙasashen Afirika da dokokin su suka haramta ɗabi'ar neman jinsi.
Dokar ƙasar da ta haramtar auren jinsi ta shekarar 2014, ta yi tanadin ɗaurin shekara 14 ga duk wanda aka kama da auren jinsi ko shiga ƙungiyoyi masu irin wannan manufa.
Dokar ta kuma haramta aikata duk wani abu mai alaƙa da neman jinsi a bainar jama'a tare da tanadin hukuncin ɗaurin shekara 10 kan duk wanda ya karya dokar.
Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam da dama sun soki wannan doka, wadda suka ce ta janyo ƙarin tsangwama da da cin zarafi da ake nuna wa masu wannan ɗabi'a.
Wani rahoton ƙungiyar kare ƴancin ɗan Adam ta Human Rights Watch ya ce dokar ta "a hukumance ana nuna wariya ga masu neman jinsi kuma lamarin ya ƙara ɓata halin da ake ciki.''
Masu raji sun bayar da rahoton yadda ake samun masu kai hari a kan masu mu'amular neman jinsi a Najeriya, kuma wasu na ganin cewa dokar da ƙasar ke da ita ce ke ruruta wutar lamarin.
Ƙasashen Afirka da dama sun ƙirƙiro dokokin haramta neman jinsi, kuma wasu sun ƙara tsaurin irin waɗannan dokoki.
Ƙasashen da suka haramta auren jinsi ɗaya a Afirka
Majalisar dokokin Burkina Faso (wadda ta ƙunshi wakilai waɗanda ba zaɓaɓɓu ba) ta amince da wata doka da ke haramta alaƙa ta masu jinsi ɗaya, kimanin shekara daya bayan majalisar zartarwar ƙasar ta amince da wani daftarin dokar iyali wadda ta haramta auren jinsi.
A baya ƙasar ta kasance cikin ƙasashe 22 daga cikin ƙasashe 54 na nahiyar Afirka da ba su haramta alaƙar masu jinsi ɗaya ba, abin da ake yanke wa masu yin sa hukuncin kisa a wasu ƙasashen.
A bara, ƙasashen Mali da Burkina Faso masu maƙwaftaka - wadanda dukkanin su ke ƙarkashin mulkin soji sun yi dakokin haramta alaƙar jinsi.
Najeriya ma na cikin ƙasashen nahiyar da suka samar da dokar haramta alaƙar jinsi.
Talla
A 2024 majalisar dokokin Ghana ta amince da dokar hukunta masu alaƙar jinsi, sai dai shugaban ƙasar bai sanya hannu a kai ba.
Uganda ce ta fi kaƙaba doka mafi tsauri kan lamarin a tsakanin ƙasashen Afirka, inda za a iya yanke wa masu alakar jinsi daya ɗaurin rai da rai.
Jamhuriyar Nijar ma tana da dokar da ta haramta wannan ɗabi'a.











