Tottenham, Chelsea, Arsenal da Man United na zawarcin Mathys Tel

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mathys Tel
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Tottenham ta amince ta biya Bayern Munich fam miliyan 50 kan matashin dan wasan gaba na Faransa Mathys Tel, mai shekara 19. (L'Equipe - in French)

Harwayau, Manchester United na shirin sayar da dan wasan Argentina Alejandro Garnacho mai shekara 20, tare da dauko Tel don taka ma ta leda (Independent)

Sai dai Tel zai fi muradin komawa Old Trafford maimakon Arsenal, ko Chelsea ko Tottenham, kuma ya na jira ya ga ko har yanzu United na muradin sa kafin ya yanke hukuncin inda zai nufa. ( Sport)

Al-Nassr na shirin sake gwajin dauko dan wasan Japan mai taka leda a Brighton, Kaoru Mitoma mai shekara 21, inda za ta kashe fam miliyan 90 kan dan wasan, wannan ne karo na biyu kuma na karshe da kungiyar ke hakilon dan wasan.(CBS Sports)

Dan wasan gaba na Sifaniya mai taka leda a Paris St-Germain, Marco Asensio, 29, na daya daga cikin masu kai hari da Aston Villa ke son daukowa kafin rufe kasuwar saye da sayar da 'yan wasan tamaula.(Mail)

Dan wasan Ingila Ollie Watkins, zai koma taka leda a kungiyar Arsenal a watan nan, sai dai har yanzu Aston Villah na son ci gaba da zaman dan wasan mai shekara 29 a kungiyar. (Mail)

Dan wasan tsakiya na Portugal, mai taka leda a Chelsea Joao Felix, 25, na daga cikin wadanda shugaban Aston Villa Unai Emery ke son dauka. (Express)

Al-Hilal ta yi gwaggwaban tayi kan dan wasan Brazil, mai taka leda a Manchester United, wato Rodrygo, 24, inda ta ke son maye gurbin Neymar mai shekara 32 da ya bar kungiyar.(Marca)

Monaco na gab da cimma yarjejeniya kan dan wasan tsakiya na Ingila mai taka leda a Ajax, Jordan Henderson mai shekara 34. (Fabrizio Romano)