Shin Arsenal na buƙatar ɗan wasan gaba a watan Janairu?

Asalin hoton, Getty Images
Ana ci gaba da alaƙanta Arsenal da buƙatar ɗan wasa mai zura ƙwallo a raga. Dole ne ƙungiyar ta ɗauki ɗan wasan gaba, idan har tana son ƙalubalantar Liverpool wajen ɗaukar kofin Premier.
To amma rashin zura ƙwallaye matsala ce?
A duka shekarar 2024, ƙungiya ɗaya ce ta zura ƙwallaye fiye da Gunners, wato Liverpool da ke kan tebur.
Arsenal ta ci kwallo 89, yayin da Liverpool ta ci 92, wadda ta yi wasanni ƙasa da na Arsenal.
Idan ka haɗa da nasarar da ta samu a kan Brentford a ranar sabuwar shekara, alƙaluma na nuna cewa duka ƙungiyoyin sun ci ƙwallo 92 daga adadin wasanni iri guda.
Hakan na nufin ƙungiyar ta zarta Man City da ƙwallo tara, sannan 11 fiye da Chelsea da ke matsayi na huɗu.
Yayin da babu wani ɗan wasan gaban ƙungiyar da ake ta tabbacin zai iya zura ƙwallo 20 ko fiye a wannan kaka, kocin ƙungiyar, Mikel Arteta na da burin samun irin waɗannan 'yan wasa.
Tawagar ƙungiyar ba ta da ƙwarin gwiwar lashe gasar, Liverpool ta ci gaba da yin nasara ba tare da Alisson da Konate da Trent da Jota na tsawon lokaci ba, yayin da Arsenal ke samun kanta cikin tsaka mai wuya a duk lokacin da ɗan wasanta ɗaya ko biyu ke jinya.









