COP27: Wata mashiya a Kenya ta bukaci a mayar da hankali kan Afirka

COP27: Wata mashiya a Kenya ta bukaci a mayar da hankali kan Afirka
An wallafa

Matasa da ke fafutukar kare muhalli a Kenya irin su Elizabeth Wathuti suna fatan taron da ake yi kan sauyin yanayi na COP27 a kasar Masar zai "yi adalci" ga mutanen da suke fama da tasirin sauyin yanayi.

Nahiyar Afirka ta yi fama da matsalolin sauyin yanayi a kwanakin baya bayan nan - kamar tsananin zafi da fari.

Ta ce "Kowa yana kiran taron da suna COP na Afirka saboda yana faruwa a nahiyar, sai dai ya kamata a kira shi da wannan suna ne saboda bukatar nahiyar Afirka ita ce ta kamata a fi mayar da hankali a kanta wajen daukar mataki".