Barcelona ta ce Sergio Roberto zai yi jinya

Sergio Roberto

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Barcelona ta sanar cewar dan kwallonta, Sergi Roberto zai yi jinya, amma ba ta fayyace ranar da zai koma buga mata tamaula ba.

Mai shekara 31 ya ji rauni a kafarsa ta hagu a minti na 15 a karawar da Barcelona ta tashi 1-1 a gasar La Liga ranar Lahadi da Getafe.

Ranar Litinin likitoci suka auna koshin lafiyar Roberto, sannan suka tabbatar da zai yi jinya.

Rashin Roberto koma baya aka samu a Barcelona, wadda za ta fafata da Atletico Madrid a gasar La Liga ranar Lahadi karawar mako na 30.

Barcelona ce ta daya a teburin La Liga mai maki 73, sai Real Madrid ta biyu mai 62 da Atletico mai maki 60 a mataki na uku.

To sai dai wani labari mai faranta rai ga Barcelona shine 'yan wasanta uku sun koma atisaye da suka hada da Ousmane Dembele da Pedri da kuma Frenkie de Jong.

Kungiyar Camp Nou wadda ta tashi ba ci a wasa da Getafe, karo na hudu a bana a La Liga da ta raba maki, wadda kwallo tara ne ya shiga ragarta a kakar nan.

Barcelona wadda ke jan ragamar teburin La Liga ta bai wa Real Madrid tazarar maki 11, kuma saura karawa tara a karkare kakar 2022/23.