Hanyoyin samun saukin migraine

An wallafa

Danna hoton da ke sama don sauraron shirin:

Wannan shirin ci gaban na makon da ya gabata ne wanda ya yi magana a kan ciwon kai mai tsanani na migraine.

A makon da ya gabata mun tauttauna ne kan abin da ya sa mata suka fi fuskantar ciwon kai mai tsanani.

Ciwon kai kan zamo alamu na wasu cututtuka, amma wannan matsancin ciwon kan da ake kira Migraine a likitance, ciwo ne na kashin kansa kuma ya fi addabar mata.

Alamomin ciwon kan sun hada da ciwo mai tsanani a bangare daya na kai, kuma yana zuwa kamar ana buga wa mutum abu ko kuma sara.

Ga wasu ya kan shafi idanunsu ta yadda ba sa gani sosai ko gani bibbiyu.Ciwon ya kan zo ne ko matsakaici ko kuma mai tsanani.

Hukumar lafiya ta Burtaniya, NHS ta ce mace daya cikin kowace biyar na fuskantar matsanancin ciwon kan a kasar.

A maza kuwa ana samun namiji daya ne cikin kowane 15 da ke fama da cutar.

Hukumar ta bayyana cewa akwai wasu abubuwa da ke tayar da ciwon ga wasu masu fama da shi, kamar misali zuwan jinin ala’ada ga wasu mata.

Matsananciyar gajiya ko wasu nau’ukan abinci ko abin sha da rashin samun isasshen barci ko matukar murna.

Alamomin cutar na iya kasancewa tare da mutum na tsawon sa’oi uku zuwa kwana hudu, inji hukumar.

Duk kuwa da cewa ana iya jin gajiya har tsawon mako guda bayan ciwon ya yi sauki.

NHS ta ce yawan shekaru na sa cutar ta yi sauki ga mafiya yawan masu fama da ita.

Amma wasu kuwa suna girma cutar na kara ta’azzara.