Rashin lantarki ya jefa ƴan Afrika ta kudu cikin ƙaracin ruwa

An wallafa

Natsuwa da kwanciyar hankali a yankunan da ke daura da birnin Pretoria na Afrika ta kudu ya faskara, bayan da suke fuskantar tsananin sautin ƙarar aikin tonon rijiyoyin fanfo.

Wannan batu ba yana nufin ƙasar ta dauki haramar lalubo wa kanta hanyar samun albarkatun ma'adanai ba ne, sai dai batu ne da ya shafi neman ƙarin albarkatun ruwa.

Cibiyoyin samar da ruwa na tuka-tuƙa masu zaman kansu, kamar wannan da ake aikin tonawa a yankin Garsfontein, suna kara yawaita a yankunan mafi arziki da ke makwabtaka da birnin kasuwancin kasar, inda ruwan famfo ke cigaba da kafewa.

"Na gaji da zama cikin yanayin rashin tabbas game da yaushe ne za mu samu ruwa da kuma yaushe ne ba za mu samu ba," a cewar wani magidanci.

"Samuwar fanfunan tuka-tuƙa da ake da su na nufin ba za mu dogara da gwamnati ba, wannnan shi ne abin da ya fi dacewa ga iyali na."

Galibin ruwan da ake samarwa a yankunan kasar sun dogara ne da amfani da lantarki da ke harbo ruwan daga manyan tashoshin ruwan zuwa manyan birane kamar Johannesburg daPretoria.

Tsananin bukatar da Afrika ta kudu ke da shi na hasken lantarki, yayin da ake samun katsewar lantarki na lokaci mai tsawo, lamarin ya yi matukar shafar aikin samar da ruwa a kasar.

"Dukkan tashoshinmu, suna buƙatar lantarki, suna buƙatar wutar lantarki. Dole ne a harba ruwa zuwa dukkan wuraren da suke bukata," a cewar Sipho Mosai, shugaban hukumar ruwa mallakin gwamnatin kasar, daya daga cikin manyan hukumomin samar da ruwa na kasar.

"Lantarki shi ne ƙashin bayan aikin da muke gudanarwa, kuma idan har ba mu da shi, zai zamo mana babbar matsala."

"Wasu lokutan nakan rasa duka ruwa da lantarki, kuma nakan shafe kwanaki cikin wannan yanayin. Matsalar tana jefa rayuwar mu ta yau da kullum cikin tsanani," Zizi Dlanga, wata mata 'yar shekaru 35, manajar wani kamfani mai zaman kansa.

Tana zaune a wani gida mai dakuna biyu a arewacin birnin Johannesburg tare da wata 'yar uwarta wacce ke aikin neman kwarewa a fannin likita.

Tace "Kudin da nake biya na ruwa ba ya sauyawa duk da irin yankewar ruwan da ake mana. Ina jin bacin rai, ba na da wata hanya ta daban na samun ruwa, wadda zai sauƙaƙa mini yanayin," a cewar Ziza.

Haƙiƙa, akwai miliyoyin 'yan Afirka ta kudu da suka shafe shekaru suna rayuwa ba tare da ruwan fanfo ba a gidajensu. Sai dai jan kafar da ake samu wajen gudanar da ayyukan samar da ruwa a yankuna yana daya daga cikin dalilan da suka sa aka shafe dogon lokaci ana fama da karancin ruwa a kasar.

"Muna cikin yanayin tabarbarewar al'amurra, tsarin samar da ruwa yana kara durkushewa," a cewar wani kwararre farfesa Anthony Turton a hirarsa da BBC.

Karancin lantarki ya kara ta'azzara al'amurra wanda rashin kyakkyawan tsarin tafiyar da kayayyakin lantarkin ya haifar, lamarin da ya haddasa mummunan yoyo, da hasarar ruwa, kana matsalolin sun haifar da gaza samar da wadataccen ruwa da ake buƙata.

Ana tafka hasarar tsaftatacce kuma tataccen ruwan sha da ya kai lita miliyan 70 a kullum sakamakon yoyon bututan ruwan da ake fama da shi a cibiyoyin samar da ruwa.

An bayyana galibin hasarar ruwan da ake samu da gazawar hukomin yankuna wajen rashin bayar da kudaden kulawa da kayyyakin samar da ruwan, mafi yawanci ana danganta matsalar da rashawa tare karkatar da kudaden don biyan bukatar kashin kai na wasu jami'ai.

Hakan na nufin tashoshin samar da ruwan ba su tsaftace ruwan yadda ya kamata.

Kuma hakan na matukar haifar da barazanar kiwon lafiya.

Cikin 'yan makonni kadan a yankin Hammanskraal, wani gari da ke wajen birnin Pretoria, cutar kwalara ta kashe mutane 29 wadanda ake tsammanin sun kamu da cutar ta hanyar ruwan sha. Ana danganta ɓarkewar cutar da rashin ingantaccen yanayin tace ruwan sha.

Lawrence Malope yana sayar da ruwan roba a gefen titin garin. Sabuwar sana'a ce da ta bulla saboda tsananin bukatar da aka jima ana nema.

Yace "Galibin mutane suna saye daga wurina saboda suna son shan tsaftataccen ruwa, saboda ruwan da ke fita daga fanfuna mai datti ne," a cewarsa.

A gida, yana tarar ruwan sama sai ya tafasa shi kafin a yi amfani da shi.

"Mutane da yawa suna kamuwa da rashin lafiya saboda ruwan da ke fitowa daga fanfunanmu kuma wasu da dama ba su san yadda ake tsaftace su ba. Muna da matasa a wannan unguwar, ina matukar damuwa game da kiyaye lafiyarmu," a cewarsa.

Amma rashin ruwan mai tsafta bai taƙaita a yankin Hammanskraal ba, wani rahoton bincike na baya-bayan nan da sashen kula da al'amurran ruwa da tsaftar muhalli ya fitar ya gano cewa, daga cikin cibiyoyin tace ruwa 155, kashi 41 bisa 100 ya nuna ba su da ingancin tafiyar ayyukansu yadda ya kamata.

Ana iya samun wannan matsala a kusan dukkan fadin kasar. A gabashin garin Makhanda, wanda aka fi sani da Grahamstown, mazauna garin sun shafe shekaru masu yawa suna fama da matsalar rashin tsaftataccen ruwan sha, sakamakon matsalar gurɓacewar yanayin da ake samu a sanadiyyar kashin dabbobi a yankin.

A lardin Free State, sakamakon wani binciken gwamnati ya gano cewa, cibiyoyin samarwa da kuma tace ruwa suna cikin wani mawuyacin hali, lamarin da ya jefa mazauna yankin cikin barazanar amfani da gurɓataccen ruwa.

A ra'ayin farfesa Turton, haduwar matsalolin rashin ruwa da na lantarki suna kara ta'azzara al'amurra a kasar.

Ya ce sakamakon matsalar hanyoyin samar da ruwa, a yanzu muna fuskantar wani mawuyacin yanayi da mutane ke mutuwa saboda cutuka."

Game da batun samar da ruwa, Mista Mosai daga hukumar samar da ruwa ya yarda cewa akwai bukatar daukar karin matakai. Ya ce kamfaninsa ya na kokarin zuba jari a fanin makamashi mai amfani da hasken rana maimakon dogaro kan hasken lantarkin kasar.

Idan ana magana game da mafita, kamata ya yi masu kudi su zuba jari wajen tona famfunan tuka-tuƙa shi ne kadai zabin da ya rage, wanda kowanne zai iya kaiwa dala $7,000 (£5,000).

Matsalar na iya haifar da gagarumin rashin daidaito a tsakanin alummar Afirka ta kudu.

"Abin da matsalar ke haifarwa shi ne kara girman giɓin da ke tsakanin mawadata da matalauta. Tana haifar da rashin adalci," a cewar Dakta Ferrial Adam wacce aiki da kungiyar wayar da kai ta WaterCAN.

Sannan akwai kuma batu na tasirin da fanfunan birtsatsen zai iya haifarwa ga muhalli ko zurfin fanfunan za su kai matakin ingancin ruwa da ya dace a yi mafani da su. A wasu daga cikin sassan kasar, ana iya samun ƙarafa masu cutarwa da kwayoyin cuta na bakteriya da za a iya samu a cikin ruwa.

Sai dai kwararru sun ce akwai abubuwan da za a yi wadanda za su amfana wa kowa kuma za su taimaka wajen daidaita matsalar gurɓacewar ruwa.

"Akwai matakai na gaggawa da za a iya dauka," a cewar Dakta Adam.

"Na farko shi ne a gyara wuraren da suke yoyo, a kashe kudaden da suka dace wajen kula da cibiyoyin samar da ruwan, kuma a dinga yin gwajin ingancin ruwa akai-akai, domin a tabbatar da ingancin ruwan da mutane za su sha."

Ta kara da cewa, ya kamata gwamnatin tarayya ta sanya ido matuka game da yadda gwamnatocin yankunan kananan hukumomi ke tafiyar da ayyukan ruwan.