Dorival Jr na shirin zama kocin Brazil bayan korar Diniz

An wallafa

Dorival Jr ya ajiye aikin horar da ƙungiyar Sao Paulo ta Brazil, inda zai kama aikin horar da tawagar ƙwallon ƙafar ƙasar.

Kulob ɗin ya sanar barinsa Sao Paulo ne a dandalin X, Twitter a baya, amma zuwa yanzu hukumar ƙwallon ƙafar Brazil CBF ba ta tabbatar da naɗin nasa ba.

"Burina ne da ya cika yanzu," in ji kociyan mai shekara 61.

Brazil ta sallami kocinta na riƙon ƙwarya Fernando Diniz a ranar Juma'a.

CBF ta matsu ta naɗa kocin dindindin yayin da Brazil take a mataki na shida a wasannin neman shiga gasar Kofin Duniya ta 2026.

Brazil ta yi canjaras da Venezuela ranar 13 ga watan Oktoba, sannan kafin haka ta yi rashin nasara a hannun Argentina, da Colombia, da Uruguay a wasannin na nahiyar Kudancin Amurka.

Dorival zai fara jan ragamar wasannin sada zumunta ne da Brazil za ta kara a watan Maris mai zuwa da Ingila, da Sifaniya a Turai.