Ten Hag zai maye gurbin Ronaldo a watan Janairu

An wallafa

Kociyan Manchester United, Erik ten Hag na fatan daukar madadin Cristiano Ronaldo da zarar an bude kasuwar saye da sayar da 'yan kwallo a Janairu.

Tun da fari Ten Hag ya ce baya son rabuwa da dan kwallon mai shekara 37, sai dai hirar da Ronaldo ya yi da Piers Morgan ta jawo dole ya hakura da shi.

A hirar da kyaftin din Portugal ya yi da Talk TV, ya ce an yaudare shi a United, kuma baya ganin martabar Ten Hag.

Hakan ya sa aka raba gari tsakanin United da Ronaldo, wanda ya yi ban kwana da Gasar Cin Kofin Duniya yana kuka a Qatar ranar Asabar, bayan da aka fitar da Portugal.

Morooco ce ta yi nasara a kan Portugal da ci 1-0 a wasan daf da na kusa da na karshe a babbar gasar tamuala ta duniya.

Tafiyar Ronaldo ta sa dole United ta nemi wanda zai maye gurbin kyaftin din tawagar Portugal, domin ta samu rarar dan wasan gaba guda daya a kungiyar.

''Za muyi dukkan abin da ya dace domin daukar fitatcen dan wasa da zai dace da mu,'' in ji Ten Hag.

Koda yake ba a fayyace wanda United za ta yi zawarci ba, ana cewa watakila Ten Hag ya bukaci Cody Gakpo, mai shekara 23 na PSV Eindhoven ko kuma dan wasan Benfica mai shekara 21, Goncalo Ramos,

Ramos ya ci Switzerland kwallo uku a wasan da Portugal ta ci 6-1 a wasan zagaye na biyu.

''Ba zan ce komai ba kan dan kwallon da zan so na dauka,'' in ji kociyan United. ''Dukkan 'yan wasa suna da kunshin yarjejeniya a tare da su, kuma ina martaba hakan.

Yana da wahala kungiya ta saki fitatcen dan wasanta a watan Janairu, kuma kowa na jiran a kammala Gasar Kofin Duniya daga nan a fara zawarci.

Kungiyar Old Trafford ta kashe kudi da dama kan fara kakar bana, inda ta dauki Antony da Casemiro da kuma Lisandro Martinez.

Sai da United za ta samu kudi da yawa a kasa, bayan ta daina biyan kudin albashin Ronaldo.