Tauraruwar da mahaifinta ya yi wa 'kisan kare mutuncin dangi'

An wallafa

Tiba al-Ali ta kasance babbar taurariyar dandalin sada zumunta na YouTube da take yin bidiyo masu daɗi da ban sha'awa game da rayuwarta.

Ta fara shafinta a kan dandanlin youtube ne a shekarar 2017 tana da shekara 17 bayan da ta bar ƙasar ta Iraki zuwa Turkiyya inda take yawan ba da labari game da 'yancin kan ta da saurayinta da abubuwan kwalliya da sauransu.

Tiba ta kasance tana yawan bayyana farin cikin ta a faifan bidyoyin ta kuma hakan ne ya janyo dubun dubatar mutane suka bi shafin nata domin kallon bidiyoyin.

Amma a watan Janairu, Tiba ta koma Iraki don ganin danginta inda mahaifinta ya kashe ta, amma kuma abin mamakin shi ne hukuncin wata shida kacal da aka yanke wa mahaifin nata.

Mutuwar Tiba ta haifar da zanga-zanga a fadin Iraki a kan dokokinta game da abin da ake kira "kisan kare mutuncin dangi", lamarin da ke nuna yadda ake mu'amala da mata a kasar da masu ra'ayin mazan jiya suka ci gaba da mamayewa.

'An Shaƙe ta cikin barci'

Tiba ta sami ƙarin mabiya shafinta sama da 20,000 tun bayan mutuwarta.

Ta kasance tana saka bidiyoyi a kullum tana nuna daɗin sabon salon rayuwar da ƙasar Turkiyya ta buɗe mata.

A cikin bidiyon ta na farko a watan Nuwamban 2021, Tiba ta ce ta koma Turkiyya ne don inganta iliminta, amma ta zabi zama a gurin saboda ta ji dadin rayuwa a can.

Rahotanni sun ce, mahaifinta, Tayyip Ali, bai amince da shawarar da ta yanke na komawa Turkiyya ba - ko kuma ta auri saurayinta, haifaffen ƙasar Syria, wanda da shi take zama a Istanbul.

An yi imanin cewa Tiba ta shiga cikin rikicin dangi lokacin da ta koma Iraki don ziyartar iyalen nata a Diwaniya a watan Janairu.

Rahotanni kuma sun ƙara da cewa Tayyib Ali, mahaifinta ya shaƙe ne da dare lokacin da take barci har ta mutu a ranar 31 ga watan Janairu. Daga baya ya mika kansa ga ‘yan sanda.

Wata mamba a karamar hukumar da aka kashe Tiba ta ce an yanke wa mahaifinta hukuncin wata shida a watan Afrilu.

Bayan kisan Tiba, daruruwan mata sun fito kan tituna a Iraki don nuna rashin amincewarsu da dokar da ta shafi "kisan mutunci".

Dokar hukunta laifuka ta Iraƙi ta ba da izinin "kisan kare mutuncin dangi" a matsayin rage laifukan cin zarafi da aka yi wa 'yan uwa, bisa ga binciken Ofishin Cikin Gida.

Dokar ta ba da damar hukunci me sassauci bisa dalilan tsokana ko kuma idan wanda ake tuhuma yana da "muradi masu daraja".

Kakakin ma'aikatar harkokin cikin gida ta Iraki, Gen Saad Maan, ya shaidawa BBC cewa ana iya kallon lamarin Tiba al-Ali a matsayin wani laifi a karkashin doka, amma kuma a wani ɓangaren ana iya ganin sa a matsayin 'kisan kare mutuncin dangi'.

Janar Maan ya bayyana cewa Tiba da mahaifinta sun yi zazzafar gardama a lokacin zamanta a Iraki, kuma 'yan sanda sun yi kokarin shiga tsakani kwana daya kafin kisan ta.

Da aka tambaye shi game da yadda hukumomi suka mayar da martani kan kisan, Janar Maan ya bayyana cewa jami’an tsaro sun gudanar da bincike cikin kwarewa tare da mika shaidun ga bangaren shari’a domin yanke hukunci.

Kisan Tiba da kuma hukuncin da aka yanke wa mahaifinta ya harzuka matan Iraki da masu rajin kare hakkin mata na duniya, wanda ke nuna rashin isasshen kariya daga cin zarafin mata da 'yan mata a cikin dokokin Iraki.

Misali, a cikin kundin hukunta manyan laifuka na Iraki, Mataki na 41 ya ba da damar "miji ya hukunta matar sa" kuma ya bai wa iyaye damar horar da 'ya'yansu cikin wasu iyakoki, kuma ana kallon haka a matsayin doka.

Mataki na 409 kuma ya bayyana cewa, idan wani ya kama abokiyar aurensa da yin zina ko kuma budurwa da saurayinta suna zina kuma ya kashe su nan take toh hukuncin sa shekaru uku ne kacal a gidan yari.

Mai fafutukar kare hakkin mata Dr. Leyla Hussein ta bayyanawa BBC cewa wadannan kashe-kashen galibi sun samo asali ne daga kiyayya ko kyamar mata da son zuciya da kuma sha'awar juya mata da jikinsu yanda aka ga dama.

Ta nanata cewa yin amfani da kalmar "kisan kare mutuncin dangi" na iya zama illa, domin a bisa kuskure yana nuna cewa wadanda aka kashe su ne ke da alhakin kashe kansu saboda aikata ba daidai ba.

A cewar Majalisar Dinkin Duniya, kusan mata da 'yan mata 5,000 a duniya ne 'yan uwa ke kashe su a duk shekara da sunan "kisan kare mutuncin dangi."

'Dole a tsayar da wannan'

Kwanaki biyar bayan mutuwar Tiba, jami'an tsaron Iraki sun hana masu fafutuka 20 gudanar da zanga-zanga a wajen majalisar koli ta shari'a a Bagadaza.

Sun rike allunan da ke cewa "A daina kashe mata" da "a dakatar da mataki 409 na cikin kundin hukunta manyan laifuka", kuma suna rera taken: "Babu wani daraja a cikin laifin kashe mata."

Ruaa Khalaf, wata mai fafutuka kuma mai kare hakkin dan Adam ta kasar Iraki ta ce: Dokokin Iraki na matukar bukatar sauye-sauye, da gyara da kuma daidaita su da yarjejeniyoyin kasa da kasa.

Ms Khalaf ta ƙara da cewa hukuncin da aka yanke wa mahaifin Tiba "rashin adalci ne", kuma tana ganin irin wadannan shari'o'in a matsayin shaida na dokokin da suka ƙeta 'yancin mata".

Hanan Abdelkhaleq, wata mai rajin kare hakkin mata a Iraqi ta ce: "Ana buƙatar a samar da mafita, dole ne a daina wannan kashe-kashen, kashe mata ya zama tamkar abu mai sauki.

"Shake mata har su mutu, caka musu wuka ya zama abu mai sauƙin yin a Iraƙi, muna fatan cewa doka za ta dakatar da mataki 409 a cikin kundin hukunta manyan laifuka, a soke matakin gaba daya."

Sauran mata masu fafutuka a shafukan sada zumunta kuma sun lura cewa kisan Tiba ba wani lamari ne boyeye ba da akwai mata da dama da aka kashe da sunan 'kisan kare mutuncin dangi' da ba a ba da rahoton su ba.

Kisan Tiba ya haifar da tattaunawa game da tsauraran dokoki don kare mata a cikin kasar da ma bayanta.

Ala Talabani shugaban kungiyar masu kishin kasa ta Kurdistan a majalisar dokokin kasar Iraki ya bayyana cewa mata a cikin al'ummarsu na fama da matsalar tsohuwar al'ada, kuma babu wata doka mai karfi ko matakin gwamnati da zai hana cin zarafin su a cikin gida, ko da kuwa yana da tsanani sosai.

Ta yi kira ga ‘yan majalisar da su amince da sabon dokar hana cin zarafi a cikin gida, wadda zai kare ‘yan uwa da mata karara daga ayyukan tashin hankali da suka hada da kisan kai da kuma cutar da su.

Majalisar Dinkin Duniya a Iraki ta yi Allah wadai da mummunan kisan da aka yi wa Tiba tare da bayyana cewa abin takaici ne cewa har yanzu ana fuskantar cin zarafin mata da 'yan mata a Iraki

Har ila yau, ta yi kira ga gwamnatin kasar Iraki da ta goyi bayan dokoki da tsare-tsare don hana cin zarafin mata da 'yan mata, da daukar dukkan matakan da suka dace don magance rashin hukunta su, ta hanyar tabbatar da hukunta duk masu aikata irin wadannan laifuffuka.

Ga mutane da yawa, labarin Tiba ya ba da haske a kan tsoffin dokokin da suka kasa kare mata daga cutarwa da cin zarafin mata a fadin duniya.

Amma ga wasu ita ma wani misali ne na abin da ake yawan rufewa da kuma dubunnan da ke gabanta waɗanda ba a taɓa ba da labarinsu ba.

Duk da haka, wasu suna ganin labarinta ɗaya ne daga cikin mutane da yawa, kuma akwai wasu mata da yawa da suka sha wahala irinta amma ba a ji labarinsu ba.