Lafiya Zinariya: Mene ne illoli da amfanin tiyatar haihuwa? 17/08 2024
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce ana ci-gaba da samun ƙaruwar mata masu juna biyun da ake yi wa tiyatar haihuwa a faɗin duniya.
Lamarin da ke nuni da cewa ana samun ƙaruwar masu juna biyun da ake yi wa tiyatar ba tare da dalilan da aka amince a yi hakan ba a likitance.
Sannan ta yi hasashen cewa idan aka ci-gaba da samun ƙaruwar zuwa shekarar 2030, gabashin Asia zai iya zama yankin da zai fi kowanne samun ƙaruwar matan da ake yi wa fiɗa don cire jarirai.
Inda yankin zai samu kashi 63 cikin dari na tiyatar haihuwa a duniya a shekarar ta 2030. Sai yankin Latin Amurka da Karibiyan da zai biyo baya da kashi 54 cikin dari, sai yammacin Asia mai kashi 50 cikin dari.
Arewacin Afrika na biye da su da kashi 48 cikin dari, yayin da kudancin nahiyar Turai zai samu kashi 47 sai Australia da New Zealand da za su samu 45 cikin dari a hasashen bincike.
Najeriya na daga cikin ƙasashen kudu da hamadar saharar Afrika, inda hasashen binciken da aka yi a shekarar 2018 ya nuna cewa, nan da shekarar 2030 za a samu ƙaruwar matan da ake yi wa tiyatar haihuwar a yankin, zuwa kashi 39 cikin dari.
Sai dai WHO ta bayar da shawarar ɗaukar matakan da za su rage yin tiyatar haihuwar da ba ta zama ta dole ba a likitance.
Binciken na shekarar 2018 ya nuna cewa damar da mata masu ciki ke samu na yi musu tiyatar haihuwar ya bambanta daga wani bangare zuwa wani na duniya.
Ƙasashe biyar,jamhuriyyar Dominican, Brazil, Cyprus, Egypt da kuma Turkiyya matan da ake yiwa fidar haihuwa sun zarta waɗanda ke haihuwa da kansu, a cewar hukumar lafiyar.
Saurari kashi na biyu na shirin Lafiya Zinariya kan amfani da illilon tiyatar haihuwa, a ƙasa.