Mutum 45 sun mutu a zanga-zangar adawa da saka hijabi a Iran

Bayanan bidiyo, Mutum 45 sun mutu a zanga-zangar adawa da mutuwar Mahsa Amini a Iran
Mutum 45 sun mutu a zanga-zangar adawa da saka hijabi a Iran
An wallafa

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Fiye da mutum 40 ne suka rasa rayukansu a jerin zanga-zangar da ake ta yi ta nuna adawa da mutuwar Mahsa Amini a lokacin da take tsare a hannun jami’an tsaro kan zarginta da rashin sa hijabi.

Duk da cewa an katse intanet a ƙasar, ana ci gaba da yaɗa bidiyon da mutane ke zargin an kashe wasu a zanga-zangar.

Ƙungiyar kare hakkin bin adam ta Amnesty ta ce a ƙalla yara huɗu jami’an tsaro suka kashe tun farkon zanga-zangar, da aka fara kwana 10 da suka wuce.