Champions League: Real za a haɗa ta da Man City ko Celtic ranar Juma'a

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar ƙwallon kafa ta Turai, Uefa za ta raba jadawalin wasannin cike gurbi a Champions League ranar Juma'a 31 ga watan Janairu.
Za a gudanar da bikin raba jadawalin a birnin Nyon, inda Real Madrid za a haɗa ta da ko dai Manchester City ko kuma Celtic ta Scotland.
Ƙungiyar Sifaniya ta kawo wannan matakin, bayan da ta kare a mataki na 12 a kan teburi, ita kuwa Celtic ta kare a matsayi na 21 da Man City ta 22.
Real ɗin za ta fara buga wasan farko ranar 11 ko kuma 12 ga watan Fabrairu, sannan ta karɓi bakuncin fafatawa ta biyu ranar 18 ko kuma 19 ga watan Fabrairu.
Daga nan ne duk wadda ta kai zagayen gaba za ta buga wasannin ƙungiya 16 da za su ci gaba da karawar.
Idan Real Madrid ta kai zagayen ƴan 16, za ta fara wasa a Santiago Bernabeu tsakanin ko dai Atlético Madrid ko kuma Bayer Leverkusen.
Daga nan Uefa za ta kara raba jadawali ranar 21 ga watan Fabrairu a Nyon, domin tantance wasannin da za a kai karawar karshe a gasar bana.
Wasannin bana da aka sauya wa fasali, za a buga fafatawar karshe a filin Bayern Munich na Allianz Arena ranar 31 ga watan Mayu.
Real Madrid ce mai rike da kofin Champions League, wadda ta doke Borussia Dortmund a bara.












