Lafiya Zinariya: Waɗanne cututtuka ne suka fi damun tsofaffi? 30/11/2024
Lafiya Zinariya: Waɗanne cututtuka ne suka fi damun tsofaffi? 30/11/2024
An wallafa
A yayin da al’ummar duniya ke samun tsawon rai, yawan tsofaffi na ƙaruwa kuma hakan na zuwa da nashi ƙalubale, musamman ta fuskar kiwon lafiya.
Yawan mutanen da suka kai shekara 60 ko fiye ya zarta yawan yara ƴan ƙasa da shekara biyar a duniya, a shekarar 2020, a cewar hukumar lafiya ta duniya.
Haka kuma, hukumar ta daga shekarar 2015 zuwa 2050, ta yi hasashen cewa yawan waɗanda ke rukunin shekarun da aka ambata a sama zai kusan ruɓanya daga kashi 12 cikin ɗari, zuwa kashi 22 cikin ɗari.
Yayin a shekarar 2050, kashi 80 cikin ɗari na masu waɗannan shekarun za a same su ne a ƙasashe masu matsakaici da ƙarancin kudin shiga.
Cututtukan da suka fi damun mutane a waɗannan shekaru sun haɗa da:
- Kurumta
- Yanar ido
- Raguwar ƙarfin ganin kusa ko nema
- Ciwon baya
- Ciwon wuya
- Ciwon suga
- Cutar matsananciyar damuwa
- Cutar mantuwa da rashin fahimtar abubuwa
- Sakewar mara da ke sanya kasa rike fitsari