'Ina yin al'amura yadda na ga dama': Fernandes ya mayar wa masu sukar sa martani

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Nick Mashiter
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport football news reporter
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 1
Kyaftin ɗin Manchester United Bruno Fernandes ya nanata cewa babu ruwansa da sukar masu suka.
Ƙwallonsa ta biyar a cikin mako ɗaya ce daga cikin 3-0 da Man United ta doke Leicester City ranar Lahadi, inda ɗan ƙasar Portugal ɗin ya yi ƙoƙari sosai.
Ya bayar an ci ƙwallo biyu sannan ya ci ɗaya kafin daga baya ya ci uku rigis a wasan da suka doke Real Socieded a Europa League ranar Alhamis, sai kuma makon da ya wuce inda ya ci ɗaya a wasansu da Arsenal.
Sai dai ƙoƙarin nasa na zuwa ne bayan tsohon ɗanƙwallon United Roy Keane ya soke shi da cewa "ba iya basirarsa kawai ake buƙata ba".
Bruno wanda tuni ya ci ƙwallo 16 da bayarwa a ci 15 a kakar nan ya yi watsi da sukar.
"Ina gudanar da al'amura yadda na ga dama," a cewar ɗan shekara 30 ɗin.
"Tabbas ba abu ne mai daɗi ba ka dinga jin irin waɗannan abubuwan a kanka, amma kuma suna iya ƙara wa mutum ƙwarin gwiwa saboda mutane na ganin za ka iya ƙara ƙoƙari.
"Ya kamata mutum ya fahimci duk da abin da mutane ke faɗi, ko ma dai a kan mene ne. Ina girmama Roy Keane sosai.
"Amma fa ba komai ne zan yi wanda zai burge kowa ba. Ina ganin girman Roy, kuma na yarda zan iya fin haka ƙoƙari a taka leda, da kuma shugabancina, da ma rayuwata."
Fernandes ya bayar da gudummawa wajen cin ƙwallo 31 a dukkan gasa a bana, inda Mohamed Salah (54) da Erling Haaland (33) suka fi shi yin hakan a gasar Premier League.










