Yadda iyalai ke neman ƴan'uwansu a kurkukun ƙarƙashin ƙasa na Syria
Yadda iyalai ke neman ƴan'uwansu a kurkukun ƙarƙashin ƙasa na Syria
An wallafa
Tun bayan kifar da gwamnatin Bashar al-Assad a Syria, mayaƙan tawayen HTS sun fitar da fursunoni da dama daga gidajen yarin ƙasar.
Cikinsu har da ƙasurgumin gidan yarin nan na Saydnaya da ya shahara wajen azabtar da fursunonin siyasa.
A wannan bidiyon, wakiliyar BBC ta ga yadda mutane ke tururuwar neman 'yan'uwansu a gidan yarin.



