Dalilin 'yan tsohuwar CPC na jaddada goyon baya ga Tinubu
Dalilin 'yan tsohuwar CPC na jaddada goyon baya ga Tinubu
An wallafa
Ƴan tohuwar jam'iyyar CPC ta shugaba Muhammad Buhari sun jaddada goyon bayansu ga jam'iyyar APC da kuma shugaba Bola Ahmed Tinubu.
A ranar Alhamis ne ƴansiyasar suka sanar da jaddada goyon bayansu ga APC da kuma shugaba Tinubu ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamnan Nasarawa Tanko Al-Makura.
A sanarwar da suka fitar sun yi watsi tare da musanta zargin rashin jin daɗin APC da kuma rahotannin da ke cewa za su fice daga jam'iyyar.
Sun yi kira ga shugabancin APC ya yi tafiya da dukkanin ɓangarorin jam'iyyar a kowane mataki.
Hon Farouk Adamu Aliyu daya daga cikin ƴan tsohuwar CPC ya bayyana matsayarsu a hirarsa da BBC inda ya ce wani ɓangare ne na CPC ari bakinsu ya ci albasa.



