Lafiya Zinariya: Hatsarin cutar tamowa ga mace mai juna biyu
Wasu bayanai da asusun tallafa wa yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, Unicef, ya fitar sun nuna cewa a lokacin da mace ke da juna biyu da kuma lokacin shayarwa tana buƙatar, ƙarfi da ƙarin sinadarai masu gina jiki.
Sai dai abincin da mata ke ci a ƙasashe da dama na duniya, na ɗauke da ganyayyaki kaɗan, kayan marmari, kifi, nama, madara da dangoginta da basu da yawa.
Kuma rashin samun wadataccen sinadaran da jiki ke buƙata ga mace mai ciki, kan janyo ta samu matsalolin kiwon lafiya kamar ƙarancin jini, cutar jijjiga, zuban jini ba ƙaƙƙautawa da matuwa.
A ɓangaren jaririn da take ɗauke da shi, matsalar tamowa ga mai ciki kan janyo jariri ya zo ba rai, ko ya zo bashi da nauyin da ya kamata a lokacin haihuwa, kuma hakan kan sa ya kaɗe ya ƙare, ko ya samu jinkiri wurin girma.
A cikin shirin Lafiya zinariya ƙwararriyar likitar yara Dr. Fatima Nasir Faskari ta bayyana cewa mata masu ciki 700, 887 ne suka kamu da cutar tamowa a Najeria, a shekarar 2024.