Ra'ayi Riga: Kan hamɓarar da gwamnatin Assad a Syria 13/12/2024

Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron shirin
Ra'ayi Riga: Kan hamɓarar da gwamnatin Assad a Syria 13/12/2024
An wallafa

Hankalin al'ummar duniya ya koma kan ƙasar Siriya, bayan a ƙarshen makon jiya, gamayyar 'yan tawaye da masu iƙirarin jihadi a ƙarƙashin jagorancin Hayat Tahrir Al-Shams, suka kifar da gwamnatin Basharul Assad, a wani yaƙin basasa da ya kwashe shekara 13.

Iyalan Assad sun mulki Syria na tsawon shekara 54, cike da zarge-zargen mulkin danniya da azabtarwa da kuma ɓatar da masu adawa da gwamnati.

Masu sharhi na cewa Bashar al- Assad ne da kansa ya ɓallo ruwan da ya kai ga kifar da shi daga mulki.

Shin yanzu, ko ina makomar Syria, wadda yaƙin basasa ya ɗaiɗaita? Me hakan yake nufi ga makomar Gabas ta Tsakiya? Wanne tasiri, wannan lamarin zai iya yi ga siyasar duniya?

Waɗannan, na cikin batutuwan da shirin ya tattauna