Wankan dawakai a teku da gasar sarauniyar kyau a Najeriya

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Zaɓaɓɓun ƙayatattun hotunan Afirka da na 'yan nahiyar a wasu sassan duniya

A ranar Asabar ne al'ummar ƙabilar Rendille na ƙasar Kenya suka gudanar da taron bukukuwan al'ada.

An yi taron nuna al'adar ne a garin Loglogo, da ke lardin Marsabit na ƙasar.

Hoton wani ɗan kasuwa ɗan ƙasar Masar, Ibrahim Abougendy a jikin madubin da aka yi da tayoyin mota a shagonsa da ke birnin Alƙahira a ranar Juma'a

Wasu matasa kenan a wajen taron Notting Hill a London ɗaude da tutar ƙasar Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo a ranar Lahadi.

Masu sha'awar wasan kwaikwayo, na manga da cosplay sun yi ado kamar yadda suke ake yi a wasan a Zimbabwe, ranar Lahadi.

Wani ɗan wasan nakasassu cikin jin daɗi da nuna ƙwarewa yana wasa da kafar roba mai launin tutar ƙasar Mauritius a bikin buɗe gasar da aka yi a birnin Paris ranar Laraba.

A Libya da zafi kan kai maki 50, wasu maza na yi wa dawakansu wanka a cikin teku a ranar Talata.

Wani mai goyon bayan babbar jam'iyar adawa ta NDC a wajen gangamin yaƙin neman zaɓen a Ghana,

Bayan shan tsangwama da ta tilastata ficewa daga gasar sarauniyar kyau ta Afirka ta Kudu, Chidimma Adetshina ta halarci taron fitar da sarauniyar kyau ta Najeriya a Lagos.

Mawaƙan sojojin ƙasar Afirka ta Kudu, da ƴan rawa sanye da kayan da aka yi da fatar damisa, sun yi waƙa a bikin kaɗe-kaɗe na soji na ƙasa da ƙasa a birnin Moscow na ƙasar Rasha a ranar Juma'a.

A ranar Talata, gomman ƴan ci rani daga Afirka ta Yamma suka isa Spain bayan tsallake hanyoyi mafiya hatsari a tekun Atlantika

A ranar Asabar a birnin Pretoria na Afirka ta Kudu, mawaƙiya KB Motsilanyane ta yi wasa a wajen bikin karramawa na Soapie.