...Daga Bakin Mai Ita tare da Awwal Marafa

Bayanan bidiyo, Latsa hoton sama ku kalli bidiyo:
...Daga Bakin Mai Ita tare da Awwal Marafa
An wallafa

Filin Daga Bakin Mai Ita na wannan makon ya karɓi baƙuncin Awwal Marafa, tauraron finafinai kuma ma'abocin shafukan sada zumunta.

Ya shaida wa BBC cewa ya samu ƙwarin gwiwar ƙirƙirar bidiyo ne a shafukan zumunta lokacin dokar kulle sakamakon annobar cutar korona.

Tauraron ya fito a finafinai kamar Sirrin Kyau, da Na Ladidi, da Labarina, da Kwana Casa'in, da Matar Aure.