Ku San Malamanku tare da Sheikh Ahmad Mahmud Izzar Sunnah

Bayanan bidiyo, Latsa alamar da ke sama domin kallo
Ku San Malamanku tare da Sheikh Ahmad Mahmud Izzar Sunnah
An wallafa

A filinmu na Ku San Malamanku na wannan mako, za mu kawo muku tattaunawa da Sheikh Ahmad Mahmud da aka fi sani da Izzar Sunnah, malamin addini a birnin Maiduguri.

An haifi shehun malamin a birnin Maiduguri kuma inda ya tafi garin Mubi da ke jihar Adamawa kuma a nan ya samu ya haddace Alƙur'ani.

Bayan nan ne kuma ya koma Maiduguri ya yi makarantar sakandire da jami'a domin samun digiri.