Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Mata sun yunƙuro wajen motsa jiki domin samun lafiya'
'Mata sun yunƙuro wajen motsa jiki domin samun lafiya'
An wallafa
Motsa jiki wani abu ne da likitoci da masana lafiya ke bayar da shawarar yi a kai a kai domin inganta lafiya da kauce wa wasu cutuka.
A baya-bayan nan wasu mata a yankin arewacin Najeriya sun fara rungumar motsa jiki, inda har ma wasu ke koyar da mutane na'ikan motsa jiki daban-daban.
A jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya wasu mata sun buɗe wuraren motsa jiki domin inganta lafiya tare da kauce wa kamuwa da wasu cutuka.