Waiwaye: Raɗe-raɗin jinyar Tinubu da barazanar shiga yajin aikin ASUU

Asalin hoton, PRESIDENCY NG
Fadar Shugaban ƙasa ta musanta raɗe-raɗin rashin lafiyar Tinubu
A farkon makon ne aka fara raɗe-raɗin cewa ba a ganin shugaban Najeriya, Bola Tinubu na fama da rashin lafiya, lamarin da fadar shugaban ƙasar ta musanta.
Tun da farko, cibiyar aikin jarida mai binciken ƙwaƙwaf ta Najeriya, ICIR ce ta rawaito cewa wasu majiyoyinta sun tabbatar mata da cewa tawagar likitocin shugaban ƙasa na ta shirye-shiryen fitar da shugaba Tinubu zuwa ƙasar wajen domin neman magani.
Cibiyar kamar dai yadda ta wallafa a shafinta na intanet ta ce "rahotanni na nuna cewa shugaba (Tinubu) na kwance a gado ba ya iya zuwa ko'ina abin da ya janyo rashin gudanar da al'amuran shugabanci. Mataimakinsa, Kashim Shettima ya wakilci shugaban a wasu ayyukan gwamnati."
An rufe Kwalejin Kimiyya da Fasaha da ke Bauchi bayan zanga-zangar ɗalibai
Haka kuma a makon ne mahukuntan Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta gwamnatin tarayya da ke jihar Bauchi suka rufe makarantar bayan wata zanga-zanga da ɗaliban makarantar suka gudanar a yau Talata.
Hukumar makarantar ta ce wasu ɓata-gari sun shiga cikin ɗaliban da ke zanga-zangar tare amfani da damar wajen neman tayar da zaune tsaye, kuma saboda hakan ne ta rufe makarantar nan take.
Kungiyar ɗaliban makarantar ta ce sun yi zanga-zangar ne game da yadda ake shiga makarantar tare da sace musu kayayyakinsu, tare da raunata wasunsu.
A daren ranar Litinin ne wasu da ake zargi ɓarayi ne suka kutsa cikin makatarantar tare da yi wa ɗaliban fashi da makami, har ta kai ga an raunata biyu daga cikinsu.
ASUU ta yi barazanar tsunduma yajin aiki

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ita ma ƙungiyar malaman jami'o'i ta Najeriya ASUU a makon ta bayyana shirinta na sake komawa yajin aiki bayan da ta zargi gwamnati da rashin cika alkawarinta na biya musu bukatunsu da suka daɗe suna nema.
Wata sanarwa da shugaban ƙungiyar, Christopher Piwuna ya fitar, ƙungiyar ta nuna damuwa kan rashin kula da walwalar mambobinta, rashin kuɗaɗen gudanarwa da kuma rashin cika alkawura da aka amince da su.
Gargaɗin na zuwa ne bayan da ministan ilimin ƙasar Dakta Tunji Alausa, ya ce "babu wata jami'a ko malaman ASUU da za su sake shiga yajin aiki a ƙasar nan." Inda ya ce za a iya ƙauce wa hakan idan aka cika alkawuran malaman da kuma shiga tattauna.
Sai dai ASUU ta ce idan ana son kauce wa yajin aiki to a cika musu alkawura da aka amince da su.
Ƙungiyar ta ce yawancin malamai na koyarwa ne ba tare da wani abu ya shiga cikinsu ba, kuma suna gudanar da bincike-bincike ba tare da samun abubuwan da suka kamata ba.
"Lamarin ya kai wasu mambobinmu ba sa iya biyan kuɗin mota zuwa wurin aiki, ba sa biya wa kansu buƙatu har ma da kuɗin makarantar ƴaƴansu," in ji ASUU.
Mutum 16 sun gudu daga gidan yarin Keffi

Asalin hoton, Nigerian Correctionals Service
A wani labarin da ya ɗauki a makon na jiya, wasu ɗaurarru 16 ne suka gudu daga gidan yarin Keffi da ke jihar Nasarawa.
Wata sanarwa da Hukumar kula da gidajen gyaran hali ta Najeriya ta fitar ta ce lamarin ya faru da safiyar Talatar ta makon jiya, kamar yadda mai magana da yawun hukumar ya bayyana.
Sanarwar ta ce wasu daga cikin ɗaurarrun da ke gidan sun ci ƙarfin maʼaikatan da ke tsaron shi, lamarin da ya bai wa mutane 16 damar guduwa nan take.
Hukumar ta kuma ce jamiʼanta biyar da ke sun samu raunuka yayin lamarin, inda biyu daga cikinsu ke cikin mawuyacin hali kuma suna samun kulawa a wani asibitin gwamnati.
Sai dai sanarwar ta ce an yi nasarar kama mutum bakwai daga cikin ɗaurarrun da suka gudu, kuma babban kwanturolan hukumar, Sylvester Ndidi Nwakuche ya ƙaddamar da bincike kan lamarin.
Tsare Tambuwal da EFCC ta yi
Mahukuntan Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta gwamnatin tarayya da ke jihar Bauchi sun rufe makarantar bayan wata zanga-zanga da ɗaliban makarantar suka gudanar a yau Talata.
Hukumar makarantar ta ce wasu ɓata-gari sun shiga cikin ɗaliban da ke zanga-zangar tare amfani da damar wajen neman tayar da zaune tsaye, kuma saboda hakan ne ta rufe makarantar nan take.
Kungiyar ɗaliban makarantar ta ce sun yi zanga-zangar ne game da yadda ake shiga makarantar tare da sace musu kayayyakinsu, tare da raunata wasunsu.
A daren ranar Litinin ne wasu da ake zargi ɓarayi ne suka kutsa cikin makatarantar tare da yi wa ɗaliban fashi da makami, har ta kai ga an raunata biyu daga cikinsu.
Mahara sun kashe mutum biyu, sun ƙona gidaje da dama a Filato
Haka kuma a makon ne wasu da ake zargin mahara sun afka wa karamar hukumar Bokkos na jihar Filato, inda suka hallaka mutum biyu tare da ƙona gidaje da kuma coci-coci.
An kai harin ne da tsakar dare ɗauke da manyan makamai waɗanda suka zarta na ƙungiyar ƴan sintiri da ke yankin.
Shugaban ƙungiyar ci gaban al'ummar Bokkos, Farmasun Fudang ya bayyana mutane biyun da aka kashe ma'ikata ne a wani coci, inda ya ce an kuma ƙona gidaje da dama da kuma coci-coci, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.
Fudang ya ce maharan sun kuma lalata gonaki sannan suka yi awon gaba da shanu da tumakai da awakai da agwagi har ma da abincin da aka adana.
"Sun zo ne ta hanyar Ding'ak da Kopmur duk da cewa akwai shingen binciken jami'an tsaro a wajen. Sojoji sun yi harbi a iska sai dai ba su fafata da maharan ba," kamar yadda Fudang ya yi zargi.
Shugaban al'ummar ta Bokkos ya ce harin na zuwa ne kwanaki biyu da kai irin makamancinsa a al'ummar Ndimar - Ya yi kira ga gwamnatin tarayya da kuma ta jihar da su kai musu ɗaukin gaggawa tare da ganin an hukunta waɗanda ke far musu.










