Yadda marigayiya Daso take taimakon marayu da masu larurar taɓin hankali
Yadda marigayiya Daso take taimakon marayu da masu larurar taɓin hankali
An wallafa
Zinaru Muhammad Giɗaɗo wadda ƙanwa ce ga marigayiya Saratu Giɗaɗo da aka fi sani da Daso ta ce haƙiƙa marigayiyar ta bar wani giɓi da har yanzu sun kasa cike shi ta fuskar jinƙai.
"Lokacin da Daso ta rasu ƙananan yara ne suka fara zuwa kan gawar suna kuka suna cewa mai ba mu abinci ta mutu."
"A duk lokacin da aka ce watan azumi ya tsaya, haka Saratu za ta shiga harkar bai wa mutane abinci da tallafa wa marayu da mahaukata."
A wannan azumin yara suka zo suka sa me ni kan batun kayan Sallah, sai na ce musu ai dama Daso ce ke ba ku yanzu kuma ba ta nan. Ni kuma ba ni da ƙarfin yin abin da take yi." In ji Zinaru Muhammad Giɗaɗo.



