Abin da ya sa asibitin Aminu Kano ya keɓe sashen kula da tsofaffi

Abin da ya sa asibitin Aminu Kano ya keɓe sashen kula da tsofaffi
An wallafa

Hukumar asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano da ke Kano ya ɓullo da sashen kula da tsofaffi a Asibitin.

Shugaban sashen Farfesa Ibrahim D Gezawa, ya ce an keɓe sashen ne domin bai wa tsofaffi kulawar da ta dace, saboda yadda matsalolinsu suka sha bamban da sauran mutanen da ba su tsufa ba.

''Sashen ya ƙushi abubuwa biyu, na farko sashen kula da su domin ba su maganin da suke buƙata, sai kuma sashen kwantar da tsofaffin idan buƙatar hakan ta taso'', kamar yassa ya yi bayani