Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda Trump ya shiga tsaka mai wuya wajen kawo ƙarshen yaƙi da Iran
Sabuwar buƙatar da Donald Trump ya gabatar game da yaƙin Iran ba ta wuce sa'o'i 24 ba ya janye ta, kuma hakan ya nuna yadda shugaban Amurkar ke fafutikar neman hanyar fita daga wani mawuyacin hali ido rufe.
A safiyar Litinin, a wani saƙo da ya wallafa a kafafen sada zumunta yana sanar da dawo da takunkumin toshe tashoshin jiragen ruwan Iran da Amurka ke aiwatarwa, ya ce duk jiragen ruwa da ke bi ta mashigar Hormuz – har da na ƙawayen Amurka – dole ne su biya haraji na kashi 20 domin mayar da kuɗaɗen da Amurka ke kashewa wajen samar da tsaro a wannan muhimmin yankin.
Sai dai washegari ya janye wannan shawara gaba ɗaya, yana mai cewa maimakon haka zai ƙulla yarjejeniyoyin kasuwanci da saka hannun jari da ƙasashen Larabawa na Tekun Fasha, inda Amurka za ta samar musu da kariya yayin zirga-zirga ta mashigar Hormuz.
Wannan sauyin matsayi na gaggawa shi ne sabon salo a rikicin da ya shafe fiye da watanni huɗu. Duk da wata yarjejeniyar fahimtar juna da aka cimma wata guda da ya gabata, wadda ta samar da tsagaita wuta na wucin gadi da tsarin tattaunawa, babu alamar cewa rikicin zai ƙare nan kusa.
Me ya Trump ya matsu ya kawo ƙarshen yaƙin Iran?
Trump na iya kasancewa ba ya son ƙara tsananta yaƙin saboda rashin farin jinin da yake da shi, yiwuwar hauhawar farashin makamashi da kuma haɗarin sabbin hare-haren Iran kan sojojin Amurka da ƙawayenta.
Haka kuma ba zai so a ƙare yaƙin ba tare da yarjejeniyar da zai iya cewa ta fi wadda gwamnatin Barack Obama ta cimma a 2015 ba.
Rosemary Kelanic, daraktar shirin Gabas ta Tsakiya na Defense Priorities, ta ce mafi yiwuwar makoma ita ce rashin wata cikakkiyar mafita.
A cewarta, rikicin ya zama "yaƙin gajiyar da juna", kuma irin waɗannan yaƙe-yaƙe kan ɗauki lokaci mai tsawo.
Yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin Amurka da Iran ta zo ƙarshe a hukumance da misalin ƙarfe 10:16 na safiyar Talata agogon Gabashin Amurka, lokacin da Trump ya sanar a shafinsa na Truth Social cewa an sake dawo da takunkumin hana jiragen ruwa na Iran shigi da fici tare da jerin sabbin hare-haren sojin Amurka a ƙasar Iran.
Iran ta mayar da martani ta hanyar ƙara kai hare-hare kan ƙawayen Amurka da jiragen kasuwanci a yankin, lamarin da ya sake kawo cikas ga zirga-zirga ta mashigar Hormuz.
Duk da nasarorin soja da Amurka ke cewa tana samu ta fuskar lalata jiragen ruwa, jiragen sama da wuraren sojin Iran, matsalar siyasa ba ta warware ba.
Har yanzu Iran na iya hana zirga-zirga
Iran, duk da rauninta ta fuskar soja, har yanzu tana iya hana zirga-zirga a mashigar Hormuz, kuma sai dai idan Amurka ta ƙara faɗaɗa ayyukan soja sosai ne za ta iya dakatar da hakan.
Shawarar Trump ta harajin kaso 20 ba sabuwa ba ce gaba ɗaya, domin ya sha ambatonta a baya.
Amma a watan da ya gabata, Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya soki irin wannan tunani lokacin da Iran ta yi magana kan yiwuwar cajin kuɗi ga jiragen ruwa masu bi ta Hormuz.
A cewarsa, dokokin ƙasa da ƙasa ba su yarda wata ƙasa ta karɓi kuɗin fito a hanyoyin ruwa na duniya ba.
Sauyin da Trump ya yi game da Hormuz ya ƙara nuna cewa ba shi da wata tabbatacciyar hanya ta warware rikicin.
Yarjejeniyar fahimtar juna ta kasance mai ruɗani da barin abubuwa da dama domin tattaunawa a gaba.
Ta kuma tanadi wata rawa ga Iran wajen kula da zirga-zirga a Hormuz tare da samar da hanyar wucewa cikin aminci ba tare da caji ba.
Yarjejeniyar ta kuma ƙunshi alƙawarin biliyoyin daloli na saka hannun jari a Iran da kuma ɗage wasu takunkuman ƙasa da ƙasa. Amma hasashen Amurka cewa hakan zai sa Iran ta daina amfani da matsayinta wajen ƙarfafa ikonta a Hormuz ya nuna bai yi nasara ba.
Wane zaɓi ya rage wa Trump?
Kelanic ta ce yarjejeniyar ta lalace gaba ɗaya domin abubuwan da ta tanada yanzu sun rushe.
A halin yanzu Iran tana sake fuskantar hare-haren Amurka kuma an katse wani muhimmin tushen samun kuɗin shiga daga man fetur.
A gefe guda, Trump yana sake fuskantar zaɓi tsakanin ƙara tsananta yaƙi ko kuma amincewa da wata mafita da za ta bar gwamnatin Iran a kan mulki.
Elliot Abrams na Majalisar Diplomasiyyar Ƙasashe ya ce tambayar yanzu ita ce: wa zai fi jurewa? Iran wadda ba za ta iya fitar da man fetur ba, ko kuwa Amurka da sauran ƙasashen da ke dogaro da man Tekun Fasha?
A ranar Talata, Trump ya samu labari mai daɗi cewa farashin kayayyaki ga masu amfani ya fara sauka.
Sai dai duk wani sabon tsanani a rikicin zai iya sake ɗaga farashin mai, wanda zai haddasa matsin lamba ga 'yan Republican yayin da ake tunkarar zaɓukan majalisar dokoki na tsakiyar wa'adi.
Bayan sanarwar Trump a Litinin, farashin gangar man fetur ya tashi da kusan kashi 10 a rana guda, mafi girman tashin da aka samu cikin shekaru shida.
A baya, takunkumin da Trump ya ƙaƙaba ya taimaka wajen matsa wa Iran lamba ta zauna teburin tattaunawa. Amma yanzu, a cewar Kelanic, tasirin Amurka kan Iran ya ragu saboda Trump ya riga ya gwada mafi yawancin matakan da zai iya ɗauka cikin sauƙi.
Sabuwar cibiyar wurin da Trump ke shirin kai wa hari
Wani sabon wurin da Trump ya ambata a matsayin inda zai kai wa hari shi ne Pickaxe Mountain, wata cibiyar binciken nukiliya mai ƙarfi kusa da birnin Tehran.
Sai dai akwai saɓanin ra'ayoyi kan muhimmancin wurin da kuma ko hare-haren sama za su iya lalata ramukan da ke da zurfi a ƙarƙashin duwatsu masu ƙarfi.
Ko da kuwa an sake komawa tsagaita wuta da tattaunawa, manyan matsalolin da suka haddasa saɓanin – kamar Hormuz, shirin nukiliyar Iran da tasirin Iran a Gabas ta Tsakiya – har yanzu suna nan.
Abrams ya ce akwai yiwuwar cimma yarjejeniya kan Hormuz, amma ba komawa ga tsohuwar yarjejeniyar fahimtar juna ba.
Yayin da yaƙin ke kusantar shiga watansa na biyar, Trump ya tunatar cewa wasu yaƙe-yaƙen Amurka, ciki har da na Vietnam, sun ɗauki shekaru masu yawa.
Amma yaƙin Vietnam ya raunana shugabancin Lyndon B. Johnson tare da lalata martabar Amurka na tsawon lokaci. Wannan wata makoma ce da Trump ke ƙoƙarin kauce wa.
Masu goyon bayansa ma sun gaji da irin "yaƙe-yaƙen da ba su da ƙarshe" a Gabas ta Tsakiya, waɗanda Trump ya sha suka a lokacin kamfen ɗinsa na shugaban ƙasa.
Amma da yarjejeniyar fahimtar junar ta rushe, tsagaita wuta ya ƙare kuma yiwuwar sabon rikici ya sake bayyana, ƙarshen wannan yaƙi bai zai kasance kusa ba kamar yadda yake tun bayan farkonsa