Mo Salah zai tsawaita zamansa a Liverpool, Madrid ta tuntuɓi Dalot

Asalin hoton, Getty Images
Ɗan wasan gaban ƙasar Masar Mohamed Salah na da niyyar amincewa da sabon kwantiragin shekara guda a Liverpool amma ɗan wasan mai shekaru 32 na ci gaba da nuna ɓacin rai kan yadda ƙungiyar ke tafiyar da tattaunawar. (Athletic)
Paris St-Germain ba ta tattauna da Salah kai-tsaye ba duk da ana alaƙanta ta da zawarcin ɗan wasan. (Sky Sports)
Real Madrid ta tuntuɓi ɗan wasan bayan Portugal Diogo Dalot, mai shekara 25, kuma an shaida mata cewa Manchester United za ta buƙaci tayin da ya kai fam miliyan 41.5, amma dai ɗan wasan Liverpool da Ingila Trent Alexander-Arnold, mai shekara 26, shi ne kan gaba a jerin sunayen ƴan wasan da zakarun na Sifaniya ke zawarci. (Relevo)
West Ham duba yiwuwar ɗaukar kocin Porto Sergio Conceicao a matsayin wanda zai maye gurbin Julen Lopetegui, wanda makomarsa a kulob ɗun ke tangal-tangal. (Guardian)
Kocin Manchester United Ruben Amorim na shirin tattaunawa da ɗan wasan gaban Ivory Coast Amad Diallo mai shekaru 22, wanda kwantiraginsa zai ƙare a bazara. (Telegraph)
Bayern Munich ta fara tattaunawa da ɗan wasan jamus Leroy Sane kan batun sabunta kwantiraginsa. (Sky Germany)
Wayne Rooney na fafutukar ci gaba da riƙe mukaminsa na kocin Plymouth Argyle bayan rashin nasara da ya samu wasannin baya bayan nan. Ana tunanin wasannin da ke tafe a gida da Oxford United da kuma Swansea City za su kasance masu muhimmanci wurin tabbatar da makomarsa. (Telegraph)
West Ham na tunanin miƙawa Vladimir Coufal sabon kwantiragi a maimakon sayar da ɗan wasan mai shekara 32. (Football Insider)
Tottenham da Newcastle United na gogayya kan ɗan wasan bayan Uzbekistan da Lens, Abdukodir Khusanov mai sahekara 20. (Telegraph)
Real Madrid na nazarin inganta kwantiragin ɗan wasan bayan Sifaniya Raul Asencio mai shekara 21. (Fabrizio Romano)
Leicester City na tunanin soke kwantiragin zaman aro na ɗan wasan Crystal Palace da Faransa Odsonne Edouard mai shekara 26 a watan Junairu. (Football Insider)












