Barcelona na son Sancho, Onana zai iya komawa Inter Milan

PA MEDIA

Asalin hoton, Jadon Sancho

An wallafa

Barcelona na sha'awar sayen Jadon Sancho na Manchester United a watan Yuni idan har za a rage mata farashinsa. Ana kuma danganta ɗan wasan na Ingila da tafiya Juventus aro. (Sport)

Shugaban Inter Milan Giuseppe Marotta ya ƙi ya kawar da yuwuwar komawar mai tsaron ragar Kamaru Andre Onana, ƙungiyar ta Serie A bayan rashin kataɓus da golan ya yi a Manchester United wadda ta saye shi a bazara. (Mail)

Sabon kwantiragin Bruno Guimaraes, a Newcastle United ya tanadi bai wa ɗan wasan na tsakiya ɗan Brazil damar tafiya Barcelona a kan yuro miliyan 65 zuwa 70. (Sport)

Leroy Sane ya zama ɗan wasan da Liverpool ke son saye na farko a ƙoƙarin da take yi na neman wanda zai maye gurbin Mohamed Salah, idan ɗan Masar ɗin ya tafi, kuma Bajamushen zai kasance wanda ya fi tsada a duk ƴan wasan da ta taɓa saye. (Mirror)

Ɗan gaban Real Madrid na Brazil Vinicius Jr, ya ce ya aika wa Jude Bellingham, sakon waya, domin ya shawo kansa ya bar Borussia Dortmund ya koma Bernabeu a bazara. (L'Equipe)

Kociyan Manchester City Pep Guardiola ya yi waya ta tsawon sa'a uku da Bellingham kafin ya tafi Real Madrid a ƙoƙarin shawo kan matashin na Ingila ya koma Man City. (Cadena Ser vdaga Goal)

Kalvin Phillips, na tunanin barin Manchester City a watan Janairu a kan rashin sa shi a wasa saboda yana ganin hakan zai iya shafar damarsa ta samun gayyata daga kocin Ingila Gareth Southgate domin buga gasar kofin ƙasashen Turai ta Euro 2024. (Mirror)

Aston Villa da Crystal Palace na daga ƙungiyoyin gasar Premier da ke lura da matashin ɗan wasan gaba na tawagar Ingila ta ƴan ƙasa da shekara 21,Jon Rowe, wanda wata 18 ya rage masa a Carrow Road yanzu. (Mail)

Matashin ɗan wasan tsakiya na Ingila Charlie Patino, mai shekara 19, yana son ya samu kwantiragi na tsawon lokaci a ainahin ƙungiyarsa wato Arsenal idan wa'adin zamansa na aro a Swansea ya ƙare. (Mail)

Barcelona na shirin sayen ɗan bayan Chelsea na Netherlands Ian Maatsen, mai shekara 21, wanda ya ƙi tafiya Burnley a bazara a kan fam miliyan 32. A watan Yuni ne kwantiraginsa zai ƙare. (Sport)

Ɗan wasan tsakiya na Manchester United Scott McTominay, zai ci gaba da zama a ƙungiyar har zuwa ƙarshen kaka, saboda kociyansu Erik ten Hag ya kawar da yuwuwar tafiyarsa a watan Janairu. Ana danganta ɗan wasan na Scotland da tafiya West Ham a bazara. (Star)