Yadda INEC ke rabar da kayayyakin zaɓen gwamna a jihar Kogi

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
Yadda INEC ke rabar da kayayyakin zaɓen gwamna a jihar Kogi
An wallafa

Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya INEC, ta ce rabar da kayyakin aikin zaɓe zuwa ƙananan hukumomin jihar Kogi da ke tsakiyar Najeriya.

Shugaban sashen ilimantar da masu kaɗa ƙuri'a na hukumar zaɓen jihar, Halliru Haruna Sule, ya ce an rabar da kayan ne a gaban wakilan jam'iyyar siyasar da ke takarar kujerar gwamnan jihar.

Ya ƙara da cewa hukumar INEC ta ɗauki matakin tabbatar da bai wa kowa damar kaɗa ƙuri'a a zaɓen gwamnan jihar da za a gudanar ranar Asabar 11 ga watan Nuwamba.