Me ya sa Kenya ta kasa kawo ƙarshen satar yara?
A 2020 ne shirin BBC Africa Eye ya bankado asirin wasu gungun masu harkallar hada-hadar satowa da sayar da yara wadanda suka farauto daga hannun mata marasa karfi da marasa matsuguni a kasar Kenya.
Daga cikin gungun akwai wasu ‘yan kwaya marasa aikin yi da kuma manyan masu shirya harkallar da kuma wasu gurbatattun ma’aikatan asibiti.
A lokacin, wakiliyarmu, wadda ta batar da kama ta samu damar shiga har cikin wasu wuraren da ke karkashin kasa da ake sayar da yaran da aka sato a kan ‘yan kudade kadan, har a Dala 400.
Bayan fitar da binciken na ‘Barayin yara’, mahukuntan kasar sun sanar da cewa gwamnatin kasar za ta dauki mataki, sannan kuma an kama wadanda suke harkallar a wuraren da ke cikin karkashin kasa.
Bayan shekara uku, wakiliyar BBC Africa Eye Njeriy Mwangi ta koma wasu daga cikin yankunan Nairobi da ake fama da talauci domin gano irin tasirin da binciken ya yi wajen hana satar kananan yaran a Kenya.
Shin an yi hukunci ga wadanda aka kama? Sannan wane irin sauyi aka samu?



