Luis Enrique ya bar aikin kociyan Spaniya

An wallafa

Luis Enrique ya bar aikin kociyan Spaniya bayan da aka fitar da kasar daga gasar cin kofin a zagaye na biyu ranar Talata.

Morocco ce ta samu galaba a kan Spaniya a bugun fenariti da ci 3-0, bayan da suka tashi minti 120 har da karin lokacin ba ci.

Kocin mai shekaru 52 ya soma jan ragamar Spaniya a shekarar 2018 kuma ya jagoranci kasar zuwa matakin kusa da karshe a gasar Euro ta kasashen Turai.

Tsohon dan kwallon Sifaniya ya sauka daga aikin horar da kasar a shekarar 2019, bayan da 'yarsa wadda ta rasu ta kamu da cansar kashi.

Daga baya ya sake karbar aiki har ya taka rawar gani a gasar nahiyar Turai a Ingila, wadda cutar korona ta kai tsaiko a lokacin.

An fitar da Sifaniya daga Euro 2020 a karawar daf da karshe, inda Italiya ta yi nasara a bugun fenariti.

Sifaniya ta casa Costa Rica 7-0 a wasan farko a rukuni a Gasar Kofin Duniya da ake yi a Qatar, sai ta tashi 1-1 da Jamus, sannan ta yi rashin nasara da ci 2-1 a hannun Japan.

A ranar Talata Sifaniya ta tashi ba ci a karawar zagaye na biyu da Morocco, daga nan aka fitar da ita a bugun fenariti.

Sifaniya ta dauki kofin duniya a karon farko a 2010 da Afirka ta Kudu ta gudanar da wasannin.

Ranar Asabar Moropcco za ta kara da Netherlands a wasan Quater finals a babbar Gasar tamaula ta Duniya.